Bayan Fitowar Sakamakon Jarrabawar POST UTME Na Kowacce Jami'a Tambayoyi Suka yawaita kan adadin MAKI Nawa ake Bukatar Kowanne Dalibi yasamu Kafin SAMUN admission a Makarantar? Dafarko Yakamata Musan Cewar Kowacce Jami'a Tanada Tsarin datake bi Wajen Bayar Da Gurbin Karatu, Wanda wajibi ne Kowanne Dalibi Sai yabi Wannan tsarin Kuma Yacika Sharudda Kafin Samun Admission. Karanta : Cikakken Bayani Gameda Inter Faculty Transfer (IFT) 1✓Dafarko Cin Mafi karancin Makin din da Jami'ar tasanya a Matsayin Cut-off Mark dinta na Jarrabawar JAMB (Kokuma Sama Dahaka ga Wasu Depertments Din) 2√Yin Jarrabawar POST UTME; Tare Da cin Mafi Karancin Makin da Jami'ar tasanya a matsayin Cut-off Mark dinta (Kokuma Sama Dahaka ga Wasu Depertments Din) 3√ Average Dinka dole yakai adadin MARK din Da'ake Bukata a Depertment Dinka, Misali kana Neman BSC. Chemistry Kuma a chemistry ana Neman 180 ne a JAMB To a karshe dole ne sai average Dinka yakai 180 Shima. Karanta : Cikakken Bayan
Da farko idan kana son ka lissafa jimillar sakamakon Jarrabawarka na Jamb dana Post-Utme (Aggregate Calculation) a binda zakayi shine zaka tara sakamakon Jarrabawarka na Jamb da sakamakon Jarrabawarka na Post-Utme guri guda, sannan ka rabasu gida biyu. (JAMB + POST-UTME) ÷ 2 Misali : Karanta : Ma'anar Deferrel tareda Amfaninsa Ga Dalibai sakamakon Jarrabawarka na Jamb shine 250 Sakamakon Jarrabawarka na Post-Utme shine 250 To sai ka tara su guri guda ka rabasu gida biyu 250 + 250 = 500 500 ÷ 2 = 250 Jimillar sakamakon Jarrabawarka ya kama 250. Karanta : Wanene Vistor a Jami'o'in Najeriya ? Abinda ya rage maka shine ka kwatantashi da a binda ake bukata a fannin karatun da kake nema, idan yakai ko kuma yafi to a binda ake bukata kenan, idan kuma bai kaiba, a Kwai yiwuwar rashin samun gurbin karatu (Admission). Karanta : Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda Jamb Regularization Shin Wannan Rubutun Ya Amfaneku ? Kusanar damu ta Comment Box domin Kara mana Karfi