Skip to main content

Abubuwan da Yakamata Kasani Bayan Kammala Jarrabawarka ta Post UTME





  Bayan Fitowar Sakamakon Jarrabawar POST UTME Na Kowacce Jami'a Tambayoyi Suka yawaita kan adadin MAKI Nawa ake Bukatar Kowanne Dalibi yasamu Kafin SAMUN admission a Makarantar?


Dafarko Yakamata Musan Cewar Kowacce Jami'a Tanada Tsarin datake bi Wajen Bayar Da Gurbin Karatu, Wanda wajibi ne Kowanne Dalibi Sai yabi Wannan tsarin Kuma Yacika Sharudda Kafin Samun Admission.

Karanta Cikakken Bayani Gameda Inter Faculty Transfer (IFT)

1✓Dafarko Cin Mafi karancin Makin din da Jami'ar tasanya a Matsayin Cut-off Mark dinta na  Jarrabawar JAMB  (Kokuma Sama Dahaka ga Wasu Depertments Din)


2√Yin Jarrabawar POST UTME; Tare Da cin Mafi Karancin Makin da Jami'ar tasanya a matsayin Cut-off Mark dinta (Kokuma Sama Dahaka ga Wasu Depertments Din)


3√ Average Dinka dole yakai adadin MARK din Da'ake Bukata a Depertment Dinka, Misali kana Neman BSC. Chemistry Kuma a chemistry ana Neman 180 ne a JAMB To a karshe dole ne sai average Dinka yakai 180 Shima.

Karanta Cikakken Bayani Gameda Intra Department Transfer (IDT)

Menene Average ?


Average Shine Sakamakon Jarrabawar ka Na JAMB Dakuma Na POST UTME idan aka Hada, sai a Rabashi Gida Biyu; Misali a, JAMB kaci 217 Yayinda a POST UTME Kuma Laci 240 to Lissafin zai Zama 217+240=457 Yayinda 457÷2=228.5

To haka Abun Yake.


Dan Haka idan de Average Dinka baikai   adadin MARK din Da'ake Bukata a Depertment Dinka ba to Kai tsaye Baka cika Sharadin Samun Admission ba a Jami'ar dakake nema, kamar Yanda Tsarin yake.


 A Karshe Menene Shawara Ga Wanda average dinsu bekai Adadin da Ake Bukata ba?

Karanta : Cikakken Bayani Gameda Inter-University Transfer  


Shawara Anan Itace Chanja Wata Makarantar da a Yanzu Bata yi Online registration ba Kokuma ake da Damar a Neman ta a Yanzu Musamman Makarantun Da'ake Degree Karkashin Affiliated Wanda Yanzu nasan sune zasufi Samuwa.


@ASOF.2021

WHATSAPP NO. 08038485677


Rubutu Mai Alaka :

Yadda Zaka Fitar da Average din Jamb da Post UTME dinka

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Abubuwa 10 Da Yakamata Ka tanada Kafin Lokacin Rijistarka ta Jamb

     Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.      Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,  domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka: 1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala). 2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yaf...