Skip to main content

Posts

Showing posts from June, 2020

Bayani Gameda Scholarship Tare Da Yadda Ake Nemansa

MENENE SCHOLARSHIP, KUMA YAYA AKE NEMAN GURBIN KARATU TA SCHOLARSHIP?   Tsari Mataki zuwa Mataki... Nagartaccen dalibi mai hazaka da ke fatan zuwa karatu a jami'o'in ƙasashen waje, Ko kuma Wasu Bangarorin Karatu Masu tsada, Wanda Koda a gida zeyi, shi ya san mahimmancin neman “Schorlarship" mafi kyau. Karanta : Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100 Shi dai tsarin Scholarship wani tallafi ne na kudi wanda ake bayarwa ta Hanyar, gwamnataci, kamfanoni da manyan Jami'o'i. Za'a iya amfani da gudunmawar da aka samu a cikin tallafin kudin wajen biyan kuɗin makaranta, samar da littattafai da kuma masaukan kwana.  Kamar yadda abun yake tallafin karatu na scholarship yana da Matukar muhimmanci musamman wajen inganta ilimi, da yawa daga cikin Daliban kwaleji ana tallafa musu ne da wanan tsari domin su cimma burin su a fagen Ilimai da suka hada kimiya da fasaha da wassanni. Karanta : Zamantakewar Matasa Schorlaship na ɗaliban duniya wato (In

Abubuwan Da Yakamata Kasani Game Da DE

Cikakken bayani Akan Direct Entry (D.E)   •Menene Direct Entry (D.E)   Direct Entry ko D.E a takaice wata dama ce ko hanya wacce idan kabita zata kaika kowacce irin jami'a dake fadin Najeriya, Sannan kuma zaka fara karatunka ne daga Aji biyu (Level 200/ UG 2), duk da akwai wasu Departments a wasu jami'o'i wadanda su idan sun baka admission din to dole daga Aji daya zaka fara (Level 1) tare da wadanda suka shiga ta hanyar Jamb. Hakanan kuma Direct Entry anayin Rijistar ta ne sau daya a shekara itama kamar JAMB, Sannan Kuma Mafi Yawancin Makarantun Basa Shirya Wata Jarrabawa, Akan D.E, Sai de Tantancewa ta internet(online screening) Dakuma Physical screening, Wasu Makarantun Kuma suna Shirya Jarrabawa, ko interview. Kamar Jami'ar Bayero a Shekarar Data Gabata ta Shirya Jarrabawa Ga Daliban Dasuke Neman Makarantar, ta Hanyar D.E Amma a Faculty Daya Kadai (Allied Science) banda Sauran. Karanta : Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100 ---Su waye Suke da Damar

Tarihin Hukumar Nabteb

YAU CIKIN YARDAR ALLAH ZAMU CIGABA DA BAYANINE AKAN JARRABAWAR NABTEB (National Business and Technical Examinations Board) Karanta : Tarihin Hukumar Jamb   Ita dai wannan jarrabawa ta NABTEB tana daya daga cikin jarrabawoyin kammala sakandire. An kirkiri Hukumar wannan jarrabawa ta NABTEB  a shekara ta (1992) karkashin tsarin Ilimi Na gwamnatin tarayya domin rage yawan cunkoso da ake samu Na jarrabawowin kammala sakandiri. Sannan wannan jarrabawa kaf Na kunshe  ne da harkokin Na (TECHNICAL ) sannan da harkokin kasuwanci,    Haka Zalika karkashin wannan hukuma ne suke shirya NATIONAL TECHNICAL EXAMINATION (NTC). Da kuma NATIONAL BUSINESS CERTIFICATE (NBC) Sai kuma babar NABTEB wato (ANBC da ANTC) Wanda zamuyi bayani akasu insha Allah. Karanta : Tarihin Hukumar Waec    Sannan itama tana da babbar daraja kamar irin su, WAEC amma sai dai ita makarantu (technical) da (business) suke yinta. Ita ba kamar WAEC da NECO bace da kowa keyin ta, sannan idan kana da shedar