• Me ake nufi da Inter Faculty Transfer ? • Yaya akeyin Transfer din ? • Kowace Jami'a tana yi ? • Menene requirements din ? _____________________________________________________________ Inter Faculty Transfer wani tsari ne da yake bawa dalibi damar canja tsangayar da yake karatu zuwa wata ta daban amma a cikin Jami'ar da yake karatun. Akwai dalilai da dama da sukan iya haddasa yin Transfer din wanda suka hada da rashin gane karatu a wannan tsangayar (Academic Performance) kokuma ba zaka iya biyan kudin karatu a wannan tsangayar ba, ko makamancin haka, to idan ya zama haka ne zaka iya yin transfer kaje inda kake ganin zaka iya. Karanta : Bayani Gameda Scholarship tareda Yadda Ake Nemansa • Yaya ake yin Transfer din ? 1• Da farko zaka rubuta letter zuwa ga Rajistara na Neman yin Transfer din amma ta hannun Department dinka zaka Rubuta letter din, (Saboda haka abinda yafi shine ka samu level Coordinator/Program Coordinator dinka kayi masa bayani to shi zaiyi guiding dinka kawai)