Skip to main content

Cikakken Bayani Gameda Inter Faculty Transfer (IFT)




• Me ake nufi da Inter Faculty Transfer ?

• Yaya akeyin Transfer din ?

• Kowace Jami'a tana yi ?

• Menene requirements din ?

_____________________________________________________________
Inter Faculty Transfer wani tsari ne da yake bawa dalibi damar canja tsangayar da yake karatu zuwa wata ta daban amma a cikin Jami'ar da yake karatun.

Akwai dalilai da dama da sukan iya haddasa yin Transfer din wanda suka hada da rashin gane karatu a wannan tsangayar (Academic Performance) kokuma ba zaka iya biyan kudin karatu a wannan tsangayar ba, ko makamancin haka, to idan ya zama haka ne zaka iya yin transfer kaje inda kake ganin zaka iya.

Karanta :Bayani Gameda Scholarship tareda Yadda Ake Nemansa

• Yaya ake yin Transfer din ?


1• Da farko zaka rubuta letter zuwa ga Rajistara na Neman yin Transfer din amma ta hannun Department dinka zaka Rubuta letter din, (Saboda haka abinda yafi shine  ka samu level Coordinator/Program Coordinator dinka kayi masa bayani to shi zaiyi guiding dinka kawai)

 2• Daganan su Kuma Academic Division zasu baka Form na transfer din saika cika, kudin sa yakan kai kusan dubu goma (N10,000)

3• Idan ka cika sai ka kaima Shugaban Department dinka form din (HOD)shine zai Cigaba da  processdin

4• Sannan form na transfer din ana fara bayar dashi ne a Second Semester, ana rufewa Kuma a ranar da aka gama Jarabawar ta Second Semester.

5• A karshe, za'a sanar maka idan an karbi transfer din naka ko ba'a karba ba 

6• Ba'a yarda kowanne Faculty (Tsangaya) ba ya bada transfer ga kashi 5% na daliban dake tsangayar

7• Sannan ba'a yin transfer din sau biyu. Idan kayi transfer sannan kuma kaga can din ma bai maka ba to shikenan saidai ka hakura kayi a hakan kokuma kabar Jami'ar.

8• Dole Sai an baka Official Letter daga Registrar shaidar cewa an yimaka transfer din.

• Kowace Jami'a tana yi?

Ehh, kowace Jami'a tana yi saidai tsarin wannan Jami'ar ya bambanta Dana wannan ne amma duka sunayi.

 Karanta :Miftahu Panda Yagodewa Asof Bisa Karramashi datayi

•Menene requirements din ?

Akwai requirements da dama kusan duka daya ne inda suke da bambanci shine wajen CGPA, ga wasu daga cikin requirements din:

1• Dole ya zama SSCE dinka Jamb dinka Faculty dinka Department dinka su zama sunada alaka da inda kake so ka koma (Ba zai yuwu Kana Sociology ka koma Cyber Security ba)

2• Dole sai ya zama Carryover dinka basu wuce 2 ba

3• Dole sai idan kai dan aji biyu ne (Level 200)

4• Kar CGPA dinka yayi kasa da 1.00 .

Rubutuka Masu Alaka :

Cikakken Bayani Gameda Intra Department Transfer (IDT)

 Cikakken Bayani Gameda Inter-University Transfer (IUT)

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak