Ganin yadda wasu daga cikin Dalibai kan fuskanci kalubale akan wannan lamari na Uploading din O'level, Wanda kuma a mafi yawan lokuta hakan kan haddasawa irin wadancan Dalibai rasa guraben karatu a Jami'o'i da sauran manyan makarantun kasarnan, yasa hukumar Jamb ta bawa Dalibai Damar Duba sakamakon Jarrabawoyinsu na O'level (SSCE) da akayi musu Uploading a Portal din hukumar ta Jamb. Ga Matakan da zakabi domin Duba sakamakon jarrabawar taka ta O'level da akayi maka Uploading a portal din Jamb, Karanta : Tarihin Hukumar Waec Matakan sune: •> Abin da zakayi da farko shine ka ziyarci shafin Hukumar jamb, Wanda ananne zakayi login (shiga) profile dinka na Hukumar Jamb, akan adireshin www.Jamb.org.ng/efacility/ •> Bayan wannan shafi yabude zakaga wasu akwatuna guda Biyu, to zaka saka E-mail Address dinka a akwatu ta farko Sannan ka saka jamb profile password dinka a akwatu ta Biyu, Sannan saika Danna mabullin Login, Wanda ke a kasa