Skip to main content

Yadda zaka Bude Profile tareda Duba sakamakon Jarrabawarka ta Jamb a Sakon Message






   Hakika Hukumar Jamb tana kawo sababbin tsaruka, tare da yin sababbin Gyare-gyare a cikin Al'amuran da suka shafi Jarrabawar, hakanne yasa Hukumar ta Jamb ta saukakawa Dalibai hanyar da zasubi wajen Bude Profile, tareda Duba sakamakon Jarrabawar tahanyar tura Sakon Kar ta kwana, a maimakon da Da sai Dalibi ya ziyarci shafin Hukumar wato Jamb portal



   A yau rubutun namu zai mayar da hankaline fagen sanar daku yadda zaku Bude Jamb profile tareda Duba sakamakon Jarrabawar ku ta hanyar tura sako batare da ka ziyarci shafinsuba, Sannan basai kaje Kafe ba, Kana daga Gida a cikin Daki zaka Bude Profile a turo maka profile code dinka, kaje kasayi E-Pin, Sannan da zarar sakamakon Jarrabawar Jamb din yafito ma zaka Iya dubashi ta hanyar message din kamar yadda ka Bude Profile ta message


    Hakika ba wasu dogayen matakai akebi ba, amma bari mudauki kowannensu muyi Bayani akan yadda zakayishi.



     •> Yadda zaka Bude Jamb profile ta Message:


    • Katabbatar da akwai Katin da Bai Gaza Naira Hamsin (#50) ba a layin naka, saboda zasu dauki Naira Hamsin da zarar katura


   • Abu na farko da zakayi shine ka shiga gurin rubuta message na wayarka,


   • Sai ka rubuta sunanka Surname First, Ma'ana sunan mahaifinka zaka fara rubutawa Sannan ka biyo da sunanka, Sannan kuma idan Kana Aiki da sunan Kakanka ko sunan Garinku sai ka rubutashi a karshe


 •  Sannan sai katura message din zuwa ga Lambar 55019


• Dazarar message din yaje za'a turo maka wasu lambobi guda Goma, wadannan lambabin da aka turo maka sune profile code dinka, ma'ana dasu zakayi amfani wajen sayen Lambobin E-Pin,

    sunada matukar muhimmanci, saboda haka kasamu Biro da takarda ka rubutasu.


    •> Nayi Kuskure a Fagen Rubuta Sunan da na Bude Jamb profile dashi, Yazanyi ?  


   Kwantar da hankalinka zaka Iya gyarawa matukar baka sayi E-Pin ba, idan kasayi E-Pin kuwa saidai kayi Green Card, ko kuma kasake layi, kasayi wata E-Pin din,



    Idan baka sayi E-Pin ba kawai ka shiga gurin rubuta message din wayarka ka rubuta  EDIT SURNAME idan a suna na Biyu kayi kuskure, idan kuwa a suna na farkone sai ka rubuta EDIT FIRST NAME, idan kuwa sunan karshene sai ka rubuta EDIT OTHER NAME, bayan ka rubuta sai ka tura zuwa Lambar da ka Bude Profile Code da ita, ma'ana 55019


   Dazarar sakonka yaje, zasu baka dama ka sake sunan da ka bukaci sakewa sai ka tura musu, dazarar yaje kuwa shikenan sunan zai canja.



 •> To, ta yaya zan Duba sakamakon Jarrabawata ta Jamb ta Message ?


    Kwantar da hankalinka yanzu Pandancy zai warware maka,


     Idan Kana bukatar Duba sakamakon Jarrabawar ka ta Jamb ta message, abinda zakayi shine ka dauko layin da ka Bude Jamb profile dashi, Sannan ka tabbatar da akwai kudi kimanin Naira Hamsin akan Layin,


 • Bayan ka Dora layin naka akan waya sai ka shiga gurin rubuta message na wayarka, karubuta RESULT


 • Sai katura zuwa Lambar 55019


    Dazarar sakonka yaje, zakaga sun turo maka sakamakon Jarrabawar ka ta Jamb, zakaga makin da kasamu a kowanne Subject, Sannan daga karshe zakaga Aggregate (Total), Wanda shine Adadin makin da kasamu a jimilla, ma'ana idan an hadasu baki Daya.



    Shin wannan rubutun ya amfaneka ?


Fadawa Abokinka / Kawarki  shima/ itama  Yazo/ tazo ya/ ta karanta, kuma kaima ka dawo.



   Kana da tambaya ?


   Sanar damu ta comment box.



    Mungode



Miftahu Ahmad Panda.



RUBUTUKA MASU ALAKA :


mdannai 9 da zakayi iya amfani dasu a madadin mouse a lokacin Jarrabawarka ta Jamb

 Tarihin hukumar Jamb


Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak