Skip to main content

Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta NECO


    Biyo bayan Sakin Sakamakon Jarrabawar NECO da Hukumar Shirya Jarrabawar tayi Shiyasa wannan Shafi Na Pandancy yaga Dacewar Yayi Rubutun da Zai nunawa Dalibai Hanyar da Yakamata Subi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu Cikin Sauki batareda shan wasu Wahalhalu ba,

    Saukakan Matakan da Zakabi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar taka ta NECO sune :

 

Karanta :Tarihin Hukumar Jamb

•> Da farko kashiga Browser din wayarka Sai Kadanna Gurin Bincike (Search) Sai karubuta Adireshin result.neco.gov.ng, Sai kadanna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken

•> Bayan Shafin Yabude Zai Baku wasu Akwatina Guda Hudu, Akwati ta Farko An Rubuta Exam Year, Abinda Ake Bukatar kasanya a cikin wannan Akwati shine Shekarar da karubuta Jarrabawar taka ta NECO Misali 2020,

ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zakuga An rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shine wacce Irin Jarrabawa kakeson Dubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External November/December, Basic Education Certificate Examination, ko Kuma Nigerian Common Entrance Examination, To a wannan Gidanne zakasaka irin Jarrabawar da Kakeson Dubawa, Misali Muce SSCE Internal June/July.

iii. Sai kuma Akwati ta Uku Wacce Zakaga An rubuta TOKEN, Abinda Ake Bukatar kasaka a wannan Akwatin sune Lambobin da kasaya a Shafin hukumar Domin Duba Sakamakon Jarrabawar taka, Misali 1630589940,

iv. Sai kuma Akwati ta Hudu Kuma ta karshe a cikin Jerin Akwatunan, Wacce zakaga an rubuta Registration Number, Abinda Ake Bukatar kasaka a wannan Akwatin itace Lambar rijistar Jarrabawarka ta Neco wacce zaka ganta a jikin Katinka Na Jarrabawa (EXAM Card), kuma Zakaga a karshenta da Akwai Wasu Haruffa Guda Biyu.

 

Karanta : Yadda Zaka Gane idan anyi Maka Uploading din O'level Result dinka a Portal din Jamb

•> Bayan Kagama Shigar da Wadannan bayanan Abu nakarshe da Zakayi shine kadanna Mabullin CHECK RESULT da Zakaga An rubuta Kuru-Kuru a Cikin Koren Gida a Karkashin Wadannan Akwatunan,

    Kana danna Wannan Mabulli Na CHECK RESULT nan da nan Sakamakon Jarrabawar ka Na NECO zai Bayyana Gamida Fitowa Dara-Dara a Fuskar Waya ko Na'urarka Mai kwakwalwa.


      Nagode

Karanta :Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

Ku cigaba da Kasancewa da Wannan Shafi namu Na Pandancy domin Cigaba da Samun Sahihan Bayanai dasuka Shafi Bangaren Ilimi da Sauran Muhimman Fannoni, Kuma Kada Kumanta kuyi Share Domin Sauran Dalibai Su ma Su Amfana.


Daga Naku A Kullum Miftahu Ahmad Panda     (08039411956). 


Rubutuka Masu Alaka :

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

 Yadda Zaka Game Idan Anyi Maka Uploading din O'level Result dinka a Portal din Jamb

Tarihin HukumarNECO

  Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta WAEC a Sakon Message

Yadda Zaka bude Profile tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka ta Jamb a Sakon Message 

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak