Skip to main content

Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Waec A Sakon Message






     Wannan tsarin yana daga Cikin sababbin tsare-tsare Da Hukumar Ta Waec Ta Samar Domin Bunkasa Harkokin Jarrabawar a Fadin Kasashe Guda 5, Da suke a Nahiyar Yammacin Afirka, Da suka hadarda Nigeria, Ghana, Sierra Leone, Gambia dakuma Kasar Liberia.



  Hakika Abin bai kebanta ga wani kamfanin layiba, Ma'ana Ko wanne irin layin Wayane dakai Daga cikin Layukan MTN, Airtel dakuma Glo, to Zaka Iya Duba Sakamakon Jarrabawar taka dashi, matukar dai Da Katin Kira Da bai Gaza Naira 30 ba a Asusun wayartaka,


Karanta :Yadda Zaka Gane Idan Anyi Maka Uploading Din O'Level Result Dinka A Portal Din Jamb

     Abin Da zakayi kawai shine :-


• Kashiga Gurin Rubuta Sakon Kar takwana ( Create New Message) Na Wayarka,

•Idan Kashiga sai ka Rubuta WAEC* Exam Number Dinka*PIN Dinka*Shekarar Da kayi Jarrabawarka


      Ga Misalin yadda Zaka Rubuta Sakon a Kasa 👇


WAEC*4230204909*224466119002*2020


• Bayan Ka Rubuta Sakon Message Din, sai katura zuwa Lambar 32327, (Za'a Cire Naira 30, Daga Cikin Asusun wayarka kafin a turo Maka Sakamakon Jarrabawar taka).


Abin Lura : Zaka sami PIN Dinka a Jikin Exam Card Dinka,


   Kuma Idan kaduba Sakamakon Jarrabawar taka Sau 3, to shikenan wannan PIN Din Da aka baka Ta kyauta Ta tashi Daga Aiki, Saboda Haka Idan kanaso ka kara Duba Sakamakon Jarrabawarka to sai dai ka sayi Waec Scratch Card.



   > Zaka Iya Duba Sakamakon SSCE Tareda G.C.E. dukka Da wannan tsarin,


Karanta :Yadda Ake Tattara Bayanai

     Yana Da Kyau Ka Lura Da Wannan 👇



A1  Na Nufin Excellent

B2   Na Nufin Very Good

B3   Na Nufin Good

C4   Na Nufin Credit

C5   Itama tana nufin  Credit

C6   Itama tana Nufin   Credit

D7   kuwa Na  Nufin Pass

E8  itama tana nufin  Pass

F9   Kuma Na nufin Fail.




Karanta :Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb A Sakon Message


     Anan Zamu Tsaya sai kuma a Rubutunmu Na Gaba,



       Shin Ya Amfaneka ?



   Sanar Da Abokinka Domin Shima yazo ya Karanta kayatattun Rubuce - Rubucen Da suke a wannan shafi Mai Albarka,


    Kar kamanta Kadanna Mabullin Share Domin Turawa 'Yan Uwa Dalibai suma su Amfana.



      Nagode



Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.



Rubutu Mai Alaka :

Tarihin Hukumar Waec

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Abubuwa 10 Da Yakamata Ka tanada Kafin Lokacin Rijistarka ta Jamb

     Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.      Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,  domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka: 1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala). 2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yaf...