Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.
Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,
domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka:
1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala).
2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yafi Inganci, Kuma Da so Samune Shima yanada kyau Yakasance da Lambar Wayarka Akayi Rijistar Email din,
Karanta : Lokacin da Yafi Cancanta Kayi Karatu
3•National ID Card/NIN NUMBER (Ka Tabbatar Cewa cikakken Sunan ka da Kwanakin Haihuwar Ka Sunyi Dai Dai) : Yanada Kyau Dukkannin Wani Ɗalibi da yake da Aniyar Rubuta Jarrabawar Jamb ta Wannan Shekarar Ya Mallaki Lambar sa ta Ɗan ƙasa (NIN) kafin lokacin dazaiyi rijistar jarrabawarsa, Saboda Wajibine Yin Amfani da Lambar a Rijistar Jarrabawar Jamb ta Wannan Shekarar, Kamar Yadda Hukumar Jamb ɗin ta Bayyana tuntuni, Kuma Yanada Kyau Katabbatar An Sanya Maka Suna da Shekarar Haihuwarka Daidai Kamar Yanda suke a Jikin Rijistar Haihuwarka (Certificate Of Birth).
4•Ka Tabbatar Cewa Kayi Jarrabawar WAEC/NECO/NBAIS/NABTEB ETC Ko kana shirin Yi : Wajibine Ga Dukkannin Ɗalibin da Zaiyi Rijistar Jarrabawar Jamb Yakasance Ɗalibin da Yakammala Karatunsa na Sakandire, ko kuma Yake Shekarar Karshe ta Kammala Makarantar Sakandiren tasa ne, domin kuwa a Wannan Ajin ne Ake Rubuta Jarrabawoyin Kammala Sakandire, Wanda Wajibine Kowanne Ɗalibi Ya Gabatar da Sakamakon jarrabawar tasa Kafin Bashi Gurbin Karatu a Manyan Makarantun Kasarnan, ko kuma Jim Kadan Bayan Bashi Gurbin Karatun
5• Ka Tabbatar Cewa Kasan Makarantar Dazaka Nema : Yanada Kyau Ɗalibi Yakammala Yanke Shawarar Makaranta tareda Darasin Yakeson Yanema Kafin Lokacin da Zai tafi Rijistar Jarrabawar sa ta Jamb,
6•Ka Tabbatar Cewa Kasan Combination Din Daya Dace Da Depertment din Dazaka Nema : Wajibine Ga Dukkannin Ɗalibin da Zaiyi Rijistar Jarrabawar Jamb ya tabbatar Yasan Darussan da Suka Dace da Kwas din da Yake Shirin nema a Jami'ar, Domin Kuwa Ɗalibai da Dama Sukan ci Maki Mai yawa a Jarrabawarsu ta Jamb, Amman Rashin Zaɓar Subject Combination dinsu daidai yakan janyo musu Rasa Guraben Karatu,
Karanta : Dabaru 13 da Yakamata Kayi Amfani dasu Domin Inganta Turancinka
7•Wajibi Ne Ɗalibi Yayi Rijistar a Cibiyar Rijistar JAMB Da'aka Amince Da’ita : Kafin Ɗalibi Yatafi Gurin Gudanar da Jarrabawarsa ta Jamb, Yanada Kyau yayi Bincike Akan Sahihan Cibiyoyin Rijistar Jarrabawar da Hukumar Jamb ta Amince dasu, Domin Gujewa Faɗawa Cikin Cakwakiyar Rasa Gurbin Karatu, Ko ma Soke Sakamakon Jarrabawar baki ɗaya daga Hukumar Jamb,
8•Wajibi Ne Ɗalibi Yayi Thumbprint Dakan Sa a Lokacin Rijistar : A Lokacin da Ake tsaka dayi maka Rijistar Jarrabawar Jamb Wajibine ka tabbatar An Dauki Hoton Ƴan yatsunka na Thumbprint, Kada kataɓa Bari Wani Yasanya Yatsarsa Yayi maka Thumbprint a Madadinka, Domin Kuwa Muddin bakai Kayi Thumbprint dakanka a Lokacin Rijistar Jarrabawar ba, to babu Yanda Za'ayi Yatsarka tahau a Lokacin da Zaka Shiga Ɗakin Jarrabawa domin Gudanar da Jarrabawar ka,
9• Wajibine Kasanya Lura Sosai a lokacin da Ake Shigar da Bayananka a Manhajar Hukumar Jamb, Domin Gujewa Yimaka Kuskure a Cikin Bayanan naka, Wanda Hakan kan Iya Jawo maka Kashe Kuɗaɗen Data Correction (Green Card),
10• Sai kuma Mai ƙurunƙus ɗin 👉 Wajibine Ga Dukkannin Ɗalibin da Yake Sha'awar yin Rijistar Jamb ya Mallaki kuɗaɗen Rijistarsa tun kafin lokacin rijistar tasa, Wannan Shine Babban Jigon Gudanar da Dukkannin waɗancan Lamuran da muka lissafo a sama, Domin kuwa Idan Babu Kuɗi to Babu Rijistarma baki ɗaya.
Karanta : Abubuwan da Yakamata Kayi Domin Samun Nasara a Jarrabawarka ko Interview
To Ƴan Uwa Yau ma Anan zamu Dakata a Wannan Darasi Namu na Yau, Kada Kumanta Kusanar da Abokananku Domin suma Suzo su Karanta,
Shin Wannan Rubutun Ya Amfaneka ?
Kasanar Damu ta Comment Box Domin ƙara Mana ƙarfin Guiwa, Haka Zalika kunada damar sanar damu, Idan kunada Buƙatar Muyi muku Rubutu Akan Wani Maudu'i da Rubutun mu baikai Kansaba.
Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy
@ASOF2021
08038485677.
Rubutuka Masu Alaka :
Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda DE
Yadda Zaka Bude Profile tareda Duba sakamakon Jarrabawarka ta Jamb a Sakon Message
Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb
Yadda Zaka Gane Idan Anyi Maka Uploading din O'level Result dinka a Portal din Jamb
Yadda Zaka Duba Tareda Karbar Admission dinka a Portal din Jamb
Comments
Post a Comment