Skip to main content

Dabaru 13 da Yakamata Kayi Amfani dasu Domin Inganta Turancinka




      

    Ganin Yadda Dalibai da Sauran Al'umma Sukan Gaza Yin Magana da Wannan Yare na Nasara, Yasa a Yau Shafinku Mai Farin Jini na Pandancy Zai koyar daku Wasu Dabaru guda 13 da zasu taimaka muku Matuka Wajen Ganin kun iya zazzaga Turanci, kamar Turawa masu Jan Kunne,



    Ga Dabarun Kamar Haka :

Karanta : Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

1•  Domin Yin Magana da Ingantaccen Turanci, a matsayinka na mai koyo yanada Kyau kadinga Amfani da Kalmomi masu Sauki fagen yin Maganarka, Kada Kace lallai sai kayi Amfani da Manyan Kalmomi, Kabi a hankali lokacin yin Magana da Manyan Kalmomin Yana tafe a nan gaba Kadan


 2• Ka tabbatar Kasan Ma'anar Dukkannin Kalmar da Zakayi Amfani da ita, kuma Yanada Kyau ka koyi Yanda ake furtata daidai


  3• Idan zakayi magana kadinga caccanza kalmomin, kada kadinga Amfani da kalma Daya a Kowanne lokaci, Misali idan Yau kayi Amfani da Kalmar Yes gobe sai kayi Amfani da Of course tunda dukkanninsu ma'anar su Daya


  4•  Kada Kadinga Jin Tsoron Furta wata Kalma,  Saboda Jin Tsoron furtata Zai hana ka furtata daidai, kadinga yin maganarka cikin kwarin gwuiwa


   5• Idan kana Magana kada kadinga Dauka cewar ba Daidai kakeba , A'a koda ana yimaka dariya ka cigaba da Maganarka, Wataran Zaka bawa wadanda Suke Maka Dariyar Mamaki


  6•Kadinga yin Amfani da Gajerun Jimloli Kuma masu kayatarwa, Saboda hakan Zai janyo hankalin masu sauraren Maganarka Sosai


 7• Kada Kaji Tsoron Magana a gaban Wanda Yafika Iya Turanci ko kuma Wani Wanda Yake Sama dakai, Kaidai kadinga Kokarin yin Amfani da kalmomin da Kake Ganin Sun dace da kafurta musu, kuma Amfanin yin magana a gaban nagaba dakai Shine : Zaka dinga Samun Gyara daga gareshi da Zarar kafurta kalma ko Jimla ba daidaiba, Wanda hakan Zai taimaka maka Matuka Wajen Inganta turancinka

Karanta : Miftahu Panda Yagodewa Asof bisa Karramashi Datayi

  8• Kada Kadinga Fushi ko Bata Rai a Lokacin da Kake magana, Saboda Murmushi da sakin fuska suna Bada taimako Matuka Wajen Furta kalamanka daidai, batareda Yawan Samun kuskureba


  9•Kadinga natsuwa sosai a duk Lokacin da Zakayi magana da Turanci, kuma Idan so samune yanada Kyau ka kasance tsaf-tsaf, Saboda Tsafta tana Kawo natsuwa Kwarai da Gaske


 10•  Idan Yakasance zakayi Magana da Turancine a Gurin da Mutane suka taru da Yawa ko Gurin Taro, Kadinga Lura Matuka da Kalmomin da Zaka Furta dakuma maganganun da zaka fada, kuma yanada Kyau kasamu masaniya Akan Irin Tambayoyin da Zasu biyo Baya, Bayan kammala jawabinka


  11• Kada ka tsawaita Maganarka a Lokacin da kakewa Al'umma Jawabi,  kadinga lura da lokaci, kuma ka dakata da Jawabanka da Zarar Kaga mutane sun fara Gajiya da Surutunka, Kada Kabari har sai sun tsayar dakai da Kansu,


  12•  Katashi tsaye kuma ka natsu a Lokacin da Zakayi wa Al'ummar da suka halarci  Wani taro Jawabi, kuma Kada kayi Kokarin Sukar Wani Saboda kalmomin cin mutunci basuda Dadi koda kuwa da Yaren Turanci aka furtasu


13• Ka lura da Yanda Kalmomin turanci suke caccanzawa daga Present tense zuwa Past tense dakuma Future tense.


Karanta : Yadda Ake Tattara Bayanai

    To Anan Zamu Dakata a Wannan Rubutu Namu na yau,


   Dafatan dai Rubutun ya Kayatar daku, Kusanar damu ta Akwatin Comment dake Kasa, Kuma Kusanar da Abokananku Domin Suma Suzo su Karanta su Amfana.



      Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy.



Karanta : Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100

Naku a Kullum : Miftahu Ahmad Panda.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak