Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2020

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Tarihin Hukumar Neco

NATIONAL EXAMINATION COUNCIL (NECO)   wannan jarrabawa an Samar da ita ne a watan April, 1999 a zamanin mulkin Gen Abdulsalam Abubakar. Karanta : Tarihin Hukumar Waec  Wannan jarrabawa ce da 'yan ajin karshe na babbar sakandire ke yin ta sannan ita jarrabawa ce ta cikin gida ma'ana ita ba kamar (WEAC) bace da Dukkanin  kasashen  yanmacin Afirka keyi. Wannan jarrabawa an yanke  shawarar samar da  itane biyo bayan yawan  faduwa jarrabawar WAEC da Dayawa daga cikin Daliban Kasarnan keyi. Karanta : Tarihin Hukumar Jamb Sannan  abinda nake son dalibai su Sani akan jarrabawar NECO shine wasu na fadin cewar idan  jarrabawar NECO kadai kayi (Ma'ana Idan bakayi Waec ba) bakada damar fita kasashen waje kayi karatu, to gaskiya zan iya cewa ba haka abin yakeba, domin kuwa da  akwai Dumbin Makarantun kasashen waje da suke daukar dalibi yayi karatu a jami'o'i da sauran manyan makarantunsu da Sakamakon jarrabawar NECO, Sannan inaso Dalibai su san cewar Sakamakon jar