Skip to main content

Tarihin Hukumar Jamb



Wannan hukuma cibiyace ta shirya jarabawar Shiga Jami'a tare da sauran cibiyoyi na ilimi a Nigeria kamar irinsu Polytechnics da Colleges, kuma mutum zaisamu damar yin jarabawar ne matukar dai ya kammala karatunsa na sakandare.

> Wace hanya akebi a shiga Jami' a kirkiri hukumar jamb ?

Kafin akirkiri wannan hukuma ta jamb, Nigeria tanada jami,o,i ne guda shida zuwa bakwai a shekarar 1974 kenan. Kowace jami,a daga cikinsu tana shirya jarabawarta ne kuma tadauki adadin daliban da sukayi Nasarar cin jarabawar. Ana cikin hakan karkashin jagorancin mulkin Chief Olusegun Obasanjo a shekarar ya kara kirkirar wasu jami,o,i guda shida (6), bayan haka kuma sai gwamnatin ta kafa wani kwamiti dazai rika kula da jarabawar ta shiga jami,a karkashin shugabancin Mr. M. S Angulu.

 

Karanta :Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

 
Bayan haka sai wannan kwamitin ya bada shawarar akafa wasu hukumomi guda biyu, wato; CENTRAL ADMISSION BOARD da kuma JOINT MATRICULATION BOARD. Gwamnatin mulkin soja na wannan lokacin ta amshi shawarorinda kwamitin ya bata inda ta kirkiri JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION BOARD, daga nan sai aka kafa hukumar a shekarar 1978, 13th February, A karkashin dokar kundin tsarin mulkin soja ta Nigeria shekarar 1978. (Decree No. 2 of the federal military government of Nigeria)
Hakanan a shekarar 1988 watan August akayi gyara a kundin tsarin mulkin sojan na Nigeria No. 2 decree, Inda aka basu iko da damar shirya jarabawar domin shiga makarantun Polytechnics da Colleges of Education a duk fadin Nigeria.
Sannan wannan gyaran (Amendments) tun lokacin aka tsarashi aka rubutashi cikin kundin tsarin mulki na soja (Decree No. 33 of 1989, Of the federal military government).
Sannan ada anayin jarabawar ta jamb ne da takarda da pencil inda ashekarar 2012 Registrar na jamb awannan lokacin (Prof. Dibu Ojerinde) ya bada sanarwar cewa yanzu jarabawar zata kasance ne ta dayan hanyoyi uku;

1• Pepar and Pencil Testing (PPT)
Inda za,ayi jarabawar da takarda da pencil

2• Dibu Based Test (DBT)
Inda za,a kawo tambayoyin a kwamputa amma sai a amsa su a takarda

3• Computer Based Test (CBT)
Shikuma anan da tambayoyin da kuma amsasu duka zai kasancene a cikin komputa din.

Hakan ya farune sakamakon wasu da dama daga cikin dalibai suna rasa sakamakon jarabawar tasu saboda bacewar takaradar da suka amsa jarabawar.
Hakazalika wannan jarabawa anayinta ne sau daya ashekara inda akowace shekara ake samun kimanin dalibai miliyan daya da suke zaunawa jarabawar. Amma awannan shekara da muke bankwana da ita (2017) an samu kimanin dalibai Miliyan daya da dubu dari bakwai da suka zauna jarabawar (1.7 Million) Kuma jarabawar tanada darasi hudu ne; 

Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb

•English Language:-
 Wanda dolene sai kowanne dalibi yayishi, saikuma sauran darasi uku dasukeda alaka da kwas (Course) dinda kakeso kakaranta a jami,ar, sannan jarabawar tana dauke da tambayoyi guda dari biyu da hamsin (250) inda English yakeda tambaya 100, sauran darusa ukun kuma sunada hamsin hamsin (50) amma awannan shekarar (2017) da muke bankwana da ita anrage yawan tambayoyin inda aka dawo dasu 180 gaba dayan darusa hudun, English aka bashi tambaya 60, sauran darusan kuma aka basu tambaya 40 sannan kuma jarabawar a shekarun baya tanada lokacine dayakai tsawon awa uku da minti goma, (3 hours, 10 minutes) amma shima anrage inda aka mayardashi awa biyu kacal, (2 hours) Sannan adadin maki din jarabawar yananan yadda yake bai canja ba wato (400 Marks). Sannan maki mafi karanci da akeso dalibi ya samu shine 180, inda a Shekarar 2007 maki din yake 160, a shekarar 2008 kuma aka karashi yazama 170, sannan a shekarar 2009 aka mayardashi 180, a shekarar 2017 kuma abun mamaki sai hukumar ta rage yawan maki din daga 180 ta dawo dashi 120, Wanda yin Hakan yasha suka daga bakin al'ummar Nigeria Wanda akarshe hukumomin Jami,o,i suka dinga Kara Maki din daga 120 zuwa yanda Suke ganin yayi Musu Dai Dai.
a Shekarar 2018 Kuma Hukumar Jamb ta Mayar da cut off marks din Zuwa 140,Yayinda a Shekarar 2019 Kuma ta Mayar dashi 160.
 So duk da haka yakamata musani kowace university tanada adadin maki dinda takeso, ya danganta ne da irin kwas dinda kakeso kakaranta. Ba lallai ne Dan kaci 160 dinba kasamu admission.

> To ko Yaya zanyi in shiga jami,a ta hanyar jamb ?

Wannan abune mai sauki, kawai abinda zakayi shine kaje ka bude profile a shafin yanar gizo na jamb din www.jamb.gov.ng daganan saikaje banki kabiya kudin Da'aka tanada na Shekarar Nan Wanda Har yanzu basu fidda ba.
 sukuma bankin zasu baka wata lamba da akecema e-pin to idan suka baka saikaje daya daga cikin ofishin hukumar ta jamb dan yimaka rajista kokuma kaje daya daga cikin centers din da hukumar ta basu lasisin yin jarabawar. Idan zakatafi saikaje da O' level dinka (Waec/Neco/Nbais/Nabteb) sannan katabbata kaci  darasin English da ilimin lissafi (Mathematics) kuma katabbata kaci darasinda yakeda alaka da kwas dinda kakeso kakaranta a jami,ar. Sannan idan lokacin jarabawar yayi zasu sanar daku, kuma katabbata   kaci maki dinda baigaza 160 Ba, (amma fa wannan na shekarar da Mike bankwana da itane 2019, yanzu bamusan yaya abun zai kasance ba a 2020) domin shine maki mafi karanci a jamb din (minimum). To idan Kayi nasarar cin jarabawar wannan shine zai baka damar da zakaje kayi Jarabwar Post-UTME (POST-JAMB) A jami,ar da kake neman admission din. Idan akayi shima kaci to jami,ar da kanema zata baka admission inda zaka fara daga aji daya, (Level 100 /Level 1 / UG 1) to shikenan ka shiga jami,a. Sannan zaka shekara hudu idan kwas din mai shekara hudu ne, ko kumashekaru biyar idan Mai shekaru biyar ne.



        Miftahu Ahmad Panda

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak