Skip to main content

Yadda Zaka Canja Password Dinka Na Shafin Hukumar Jamb





   

      Dalibai da Dama Sukan Bukaci Canja Kalmominsu Na Sirri (Password) Bayan Kammala Rijistar su ta Jarrabawar Jamb UTME ko DE, Saboda Lambobin  123456 da Ake Sanyawa Mafi Yawan Daliban a Matsayin Profile Password dinsu yayi Rauni da Yawa, Kuma Bazaiyi Wahalar shiga ga Kowanne Mutum ba koda kuwa ba Asalin Mai Profile din bane, Dan haka Canja Lambobin zuwa wasu lambobi ko Kalmomin da Kake Bukata kuma Sukafi Sirri Abune da Yakamata Kowanne Dalibi Yayi,



     Wannan Dalilin ne Yasanya A Yau Muka Dauko Wannan Maudu'in Domin Bajeshi a Fefe, tahanyar yin Bayani Mataki - Mataki Gameda Yadda Dalibi Zai Canja Lambobin Password din nasa,


Karanta : Abubuwan da Yakamata Kayi a Ranar Jarrabawarka


      Dan Haka Batareda Wani Bata Lokaci ba Bari Na Lissafo muku matakan da Zakubi Domin Canja Lambobin sirrin naku daga 123456 zuwa Lambobi ko Kalmomin da kuke Bukata kuma sukafi muku tsaro, Muje Zuwa Ga Matakan Kamar Haka 👇:



 • Abu na farko da Zakayi Shine Kabude Browser din Wayarka Sai Kashiga Shafin Login na Hukumar Jamb tahanyar Sanya Adireshin Jamb.org.ng/efacility/, Bayan Kasanya Wannan Adireshin Sai Kadanna Mabullin Search,



  • Bayan Yabude Kai tsaye Shafin Zai baka Wasu Akwatuna Guda Biyu, Akwati ta Farko An Rubuta Email Address, to Ana Bukatar kasanya Adireshin Email din da Akayi maka Rijistar Jamb dashi, Sai kuma Akwati ta Biyu da Aka Rubuta Password,  Abinda Ake Bukatar Kasanya a wannan Akwati sune Lambobinka na Sirri (Wanda a Mafi Yawan lokuta basa Wuce 123456) Amman koda Basu bane to Password dinka dai Ake Bukatar kasanya a Gurbin, Bayan Kasanya Wadannan Bayanai sai Kadanna Mabullin Login dake ƙasan Akwatunan, Kamar Yadda Kuke Gani a wannan Hoton dake Kasa :



Karanta : Cikakken Bayani Gameda Jami'a tareda Dalilan da Suka Sanya Ake Tsoron Auren Macen Dake Jami'a

   • Bayan Shafin naka Yabude daga Sama zakaga Yana Yimaka Lale Marhaba, kuma Zakaga Sunanka tareda Profile Code din da Kabude Profile dashi, daga Kasansu kuma Zakaga Wani Mabulli da Aka Rubuta My Profile sai Katabashi,



   •Bayan Yabude Zakaga Sunanka daga Sama, daga Bangaren Hannunka na Dama Kuma Zakaga An Rubuta My Documents Cikin Jar Kala, Daga Bangaren Hannunka na Hagu Kuwa Change Password Zakaga An Rubuta Cikin Koriyar Kala, Sai Katabashi,


  

   • Bayan Yabude Zai Baka Wasu Akwatuna Guda Uku, A cikin Akwatin Farko Zakaga An Rubuta Current Password, Abinda Ake Bukatar Kasanya a Cikin Wannan Akwatin Shine Password din da kake Aiki dashi a Wannan lokacin, Sai kuwa Akwati Ta Biyu Zakaga An Rubuta New Password, Abinda Ake Bukatar Kasanya a wannan Akwati shine Sabon Password din da kake son Sanyawa a Profile din naka, Ma'ana Wanda Kakeson Ya Maye Gurbin Tsohon da Zaka Canja, Sai kuma Akwati ta karshe, Wacce Zakaga An Rubuta Confirm New Password, Ana Bukatar ka kara Sanya Sabon Password din da Kakeson Sanyawa a Cikin Wannan Akwati, Daga nan Kuma Sai kadanna Mabullin Change Password, Wanda Zakaga An Rubutashi Dara-Dara Cikin Koriyar Kala a Karkashin Wadannan Akwatuna kuma Zakaga hoton Alamar Kuba daga Bangarensa na Hagu,



   • Bayan Kuma Kadanna Wannan Mabulli nan da nan Zakaga Yarubuto maka Password Change Was Successful, to Shikenan Password dinka Yacanja, Idan Katashi zaka sake dawowa Cikin Profile din ka sai kayi Amfani da Sabon Password din da Kasanya, Kuma Idan Kanason ka ƙara Canjawa ma, Wadannan Matakan sune dai zaka Sake Bi.

    Ku lura da Wannan Hoton dake Kasa :



Karanta : Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta Waec a Sakon Message

      Shin Wannan Rubutun Ya Amfaneka ?, Sanar damu ta Comment Box Domin ƙara mana ƙarfin Gwuiwa, Kuma kada Kamanta Kasanar da Abokinka Domin Shima Yazo Ya karanta,



       Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy



Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.


Rubutuka Masu Alaka : 

Yadda Zaka Bude Profile tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka ta Jamb a Sakon Message

Yadda Zaka Gane Idan Anyi Maka Uploading din O'level Result dinka a Portal din Jamb

Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawarka ta Jamb

Yadda Zaka Duba tareda Karbar Admission dinka a Portal din Jamb

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak