Masu Bibiyar Wannan Shafi namu na Pandancy dake Kawo muku Sahihan Bayanai tareda Wayar dakai akan Lamuran da Suka Shafi Ilimi Assalamu'Alaikum, A yau Darasin namu Zaiyi Bayanine Akan Abubuwan da Yakamata Dalibi Yayi a ranar da Zai rubuta Jarrabawarsa, Bayan Dalibi Ya Karanta Littattafansa a Lokacin da ranar Jarrabawarsa take Gab da zuwa, to a Ranar Jarrabawar ma da Akwai Wasu Muhimman Abubuwa da Yakamata Yagudanar Domin Yin Jarrabawarsa Cikin Nasara,
Masu Karatu Batare da Nacika Ku da Dogon Surutu ba, Ga Jerin Abubuwan da Yakamata Dalibi Yayi a Ranar da Zai Gudanar da Jarrabawarsa :
Karanta : Zamantakewar Matasa
• A ranar Da Zaka Gudanar da Jarrabawarka Yanada Kyau Katashi da Wuri, Kayi wanka tareda Goge Haƙoranka su fita fes, Saboda Kasancewarka tsaf-tsaf Zai taimaka maka fagen Samun Natsuwa a Dakin Jarrabawa,
• Kacika Cikinka Taf da Abinci kuma kasha ruwa, Amman kada kayi Irin cin da Zaka Cutar da Kanka, Sannan Sai kasanya Tufafinka Masu Kyau tunda Cikin Jama'a Zaka Shiga,
• Kasanya a Ranka cewar Wannan Jarrabawar da zaka tafi Abune da yashafi gina rayuwarka, saboda haka yanada Kyau ka dauki Abin da Muhimmanci a Ranka, kuma Yanada Kyau kasanya Fata da Burin Samun Nasara a Zuciyarka,
Karanta : Wanene Visitor a Jami'o'in Najeriya ?
• Yanada Kyau kafita zuwa Gurin Jarrabawarka, Dazarar Lokacin Jarrabawar Yaƙarato, a kalla da Awa Daya, Idan a garinku zakayi Jarrabawar, Idan kuwa a Wani Garinne zaifi Kyau ka kwana a can, Saboda Gudun Makara,
• Ka Dauki Kayayyakin Rubutu da Sauran Abubuwan da Ake Bukata a Lokacin Gudanar da Jarrabawa, a kalla Kowanne Abu Yakasance kanada guda Biyu, haka zalika kada kamanta ka Dauki Takarda Domin Gudanar da Rough Work,
• Ka guji Aron Wani Abu Bayan Kashiga Dakin Jarrabawa, kuma Ka guji Tambayar Abokinka Wani Abu, kuma kada Kadinga Leken Abinda nakusa dakai yake Rubutawa, Kadogara da Abinda Kasani kada Kace Sai ka kwafi Amsar Wani Sannan Zakaci Jarrabawa,
•Kai tsaye Katafi Gida da Zarar Kafito daga Dakin Jarrabawar, Kada Ka tsaya yin Shira da Surutai da Abokai, Kayi tafiyarka Gida ka cigaba da Addu'a, tareda Jiran Sakamakon Jarrabawarka
Karanta : Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda Jamb Regularization
Yau ma Anan Zamu Dakata a Rubutun namu, Dafatan dai Rubutun Yakayatar Daku,
Kusanar damu ta Comment box, idan kunada Bukatar Rubutu akan Wani Abu da Yake Shige Muku Duhu a Bangaren Ilimi.
Kuma Kada Kumanta Kusanar da Abokanai tareda Ƙawayenku Domin Suma Suzo Su Karanta.
Muna Godiya bisa Bibiyar shafinmu da kukeyi
Naku a Kullum : Miftahu Ahmad Panda.
Rubutuka Masu Alaka :
Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu
Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb
Abubuwan da Yakamata Kayi Domin Samun Nasara a Jarrabawarka ko Interview
Dabaru 13 da Yakamata Kayi Amfani dasu Domin Inganta Turancinka
Lokacin da Yafi Cancanta Kayi Karatu
Manyan Dalilan da Suke Sanya Dalibai Faduwa Jarrabawa tareda Bayani Akan Yadda Zaka Guje Musu
Comments
Post a Comment