Skip to main content

Zamantakewar Matasa












ZAMANTAKEWAR""MATASA
             Kashi Na 01.

Zamantakewar Matasa Cike take Da Ababen Kalubale Dayawa Wanda Ya Shafi, Batun Neman Sana'a, Karatu Dakuma Soyayya, Da Aure.

Wannan Shiri Da Jaridar Mikiya ta Dauki Nauyin sa, Karkashin Dalibai  Ma rubuta a Bangaren Sociology Da Islamic Studies, Manufar Shirin itace Samarwa Matasa Mafita a Rayuwar Su ta Hanyar Basu Shawarwarin Dasuka Dace Da Zamanin Da muke Ciki.




Karanta : [ Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane a Duniya ?

""" MECECE ZAMAN TAKEWA"""
Zamantakewa na nufin tarayyar dan Adam, tsakaninshi da mutane yan uwansa da abokansa, kama daga lokacin da yake cin kuruciyar sa har girmansa,

Zamantakewa na farawa ne daga kuruciyar yaro, Sannan ya shiga samartaka har i zuwa dattijantaka , Alakar mutum da sauran yan uwanshi, ke nuna cikakkiyar dabi'ar Sa, yayin da yake ma'amalantar su ta Hanyar yin Magana da Aiki.

Dayake Muna Magana ne akan zamantakewar Matasa a Kasar Hausa Baki Daya, a Yau Zamuyi Duba da Sha'anin Sana'a ne a zamantakewar Matasa Wanda kowa Yasani Aikin Yi ko Sana'a Ga Matashi Shine Jigon Rayuwar sa.

a Da Can Baya kowanne Matashi Kan Tasowa Ne da Sana'ar gidan Su Misali; Dinki, Saka, Rini Dss.

Amma a Wannan Zamanin Damuke Ciki Babban Kalubalen Dayafi Ciwa Matasa Tuwo a Kwarya Shine Rashin Sana'a Kokuma aikin Yi,
Wannan Matsalar itace take Yin Tarnaqi Ga Rayuwar Matasa ta Bangorori Biyu;
Masu Muhimmanci Ga Rayuwar kowanne Matashi.

Nafarko Bangaren Karatun Sa
Nabiyu Bangaren Zamantowar Sa Cikakken Mutum ta Hanyar yin Soyayya Da Aure.

Sanin kowa ne Dukkan Abunda Muka Lissafa a Sama Abubuwa Ne Dake Buqatar kudaden Shiga Su kuwa Kudaden Shiga Basa Samuwa Sai da Aikin Yi Kokuma Sana'a.

So Dayawa matasa Mata Kan Korafin Rashin Fitowar Samarin su a Maganar Aure Dazaran Sunyi Musu Maganar Aure Sai Ruga a Guje Ba zasu Kara Ji ko Ganin Su ba, Yayinda Sukuma Matasa Maza Ke Kare Kansu Da Cewar Basu da Sana'ar Daza Su Iya Daukar Dawainiyar Soyayya Kokuma Aure, Amma a Zahiri Yake Matasan Kan Son Soyayyar da Auren Sai dai Kash Rashin kudaden Shiga Ne ke Kawo Musu Cikas.

Haka abun Yake Ma a Bangaren Karatu Musamman Ga Wanda iyayen Sa Su ka Zama Masu karamin Karfi Kokuma Suka Rigamu Gidan Gaskiya.




Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

""""a'ina Gizo Yake Sakar?

Mai Karatu Mu kasance Tare Daku a Shirin zamantakewar Matasa Na Ranar Juma'a Mai Zuwa Wanda Gungun Dalibai a Sociology Da Islamic Study Suke Gabatar Wa.

Domin Shawarwarin Ku Ko Buqatar Tattaunawa Daku Ku Tuntube Mu ta👇
Email:📧Zamantakewarmatasa@gmail.com

Ko Ta Whatsapp:07026746193



Karanta : Tarihin Hukumar Neco



Daga Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak