Skip to main content

Manyan Dalilan da Suke Sanya Dalibai Faduwa Jarrabawa tareda Bayani Akan Yadda Zaka Guje Musu





      Dalibai da Dama Sukan Fadi Jarrabawar Karshe ta Kammala Makaranta ko kuma Aji, Alhalin Sunci Jarrabawarsu ta Zangon Farko da na Biyu, ko kuma Sunci Dukkannin Jarrabawoyin da suka Gudanar a Makarantar ma Baki Daya,



      •Shin Meyake Jawo Hakan ?


    > Kokarine Basudashi ?


            Ko kuwa 


   • A ina Matsalar take ?


Karanta : Tarihin Hukumar Nbais

    > Hakika Ƙoƙarin Mafi yawan  Ɗalibai Yakan ragu, haka Zalika Irin Nasarar da suke Samu a Jarrabawoyinsu ma Sukan Ja Baya, Dazarar Aski Yazo Gaban Goshi, Ma'ana Idan Suka Bude Ido suka Gansu a Babban Aji Wanda Dagashi Zasu Kammala Makaranta, ko kuma Idan suka tsinci Kansu  a Zangon Karatu na Karshe Wanne dagashi Zasu Kammala Ajin da suke su tsallaka Aji na gaba, Wanda Wannan Shine Babban Dalilin da Kansa Daliban Faduwa Jarrabawoyinsu, 



    •Mafita Anan Itace Yanada Kyau Dalibai  su dinga Mayar da Kai Akan Karatunsu, kuma Su Guji Daina Bibiyar Littattafansu tareda Kama Sharholiya Da Zarar sun kusa Kammala Karatunsu, Wanda wannan Itace Dabi'ar Mafiyawan Daliban Wannan Zamani,


Karanta :Tarihin Hukumar Neco

    > Dalili Na Biyu Dakansa Irin Wadannan Dalibai Faduwa Jarrabawoyinsu kuwa Shine Fitowar Abinda Ba'a koya musu ba a cikin Jarrabawar : Tabbas hakan tana faruwa, Domin kuwa Jarrabawar Karshe Jarrabawace da takan hado Dukkannin darussan da aka koyawa Dalibi a Daukacin Aji ko Makarantar da Yake Gab da Kammalawa, Wanda hakan Yakan Bada Damar Ayi Masa Tambayoyi daga Cikin Dukkannin Darussan da Aka Koya masa a Wannan Ajin ko Makarantar Baki Daya, Wanda Idan Dalibai basuyi  Sa'a ba har Darussan da Ba'a koya musu bama Sukan Iya Fitowa a Takardar Jarrabawar tasu, Tunda Mafi Yawan Hukumomin Shirya Jarrabawa tareda  Malamai suna yin Amfani da Teaching Syllabus ne Wajen Tsara Tambayoyinsu ga Dalibai,



   • Mafita Anan Itace Yanada Kyau Dalibai su dinga Bibiyar Darussan da Aka Tsara Koya Musu tareda Bincike Akai ta hanyar littattafai da Yanar Gizo, Dukkannin Darasin da Suka Gani a Syllabus suyi Kokarin Bincike Akansa Domin su Fahimceshi koda kuwa Ba'a Koyar dasu Darasin a Aji ba, Saboda Su Hukumomin Shirya Jarrabawa bazasu San Ba'a koya maka Shiba, Saboda haka Zai iya fitowa a Jarrabawa, A Bangaren Malamai kuwa Yanada Kyau suma su kasance Masu Kokarin Cika Alkawurran da Suka Dauka, ta hanyar koyar da Daliban su Dukkannin Darussan da Hukumar Ilimi ta Bada Umarnin a Koyar dasu, Hakanne Zai kawo Karshen Wannan Matsala.


Karanta : Tarihin Hukumar Waec

    Anan Zamu  Dakata a Wannan Rubutu namu na Yau, 


    

    Shin Rubutun Ya Ƙayatar daku ?


    

   Kusanar damu ta Comment box Domin Kara Mana Kwarin Gwuiwa, Kada Kumanta Kusanar da Abokananku Domin Suma Suzo su Karanta.



       Mungode Da Ziyartar Shafin Pandancy



    

   Naku A Kullum  : Miftahu Ahmad Panda.


Rubutuka Masu Alaka :

Abubuwan da Yakamata Kayi Domin Samun Nasara a Jarrabawarka ko Interview

Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

Dabaru 13 da Yakamata Kayi Amfani dasu Domin Inganta Turancinka

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak