Skip to main content

Tarihin Hukumar Waec









An kirkiri  Hukumar WAEC ne A lokacin da akayi wani Taro Kan Makomar ilimi a kasashen "Yammacin AFIRKA" Wanda yahada wakilan Makarantu da dama, daga cikin wakilan Makarantun da suka halarci wannan tattaunawa Akwai :-


1- Wakili daga University of Cambridge Local Examinations Syndicate.


2- Sannan Akwai wakili daga University of London School Examinations Matriculation Council


3- Sannan akwai wakili daga West African Departments of Education.


Sunyi taronne a Shekarar 1948, Inda suka tattauna akan makomar ilimin Yammacin  Afirka.


   Inda Suka kira taron da Suna  "Tattaunawa kan makomar ilimi a kasashen Yammacin Afirka"


     A karshen taronne ma kuma suka  nada Dr. George Barker Jeffery( Wanda Darakta ne a University Of London Institute Of Education, a wancan lokacin) a matsayin Wanda zai ziyarci wasu daga cikin Kasashen Afirka, domin yaganewa idonsa halin da ilimi yake ciki a kasashen, tareda Samar da rahoto akan hakan.


   Inda  'Jeffery' yakai ziyara  ta tsawon, wata uku daga (watan Disambar 1949 zuwa watan March na Shekarar 1950),

  Kasashen da ya ziyarta sun hadar da Kasar Ghana, Gambia, Sierra Leone, dakuma Kasar Najeriya,


   Inda bayan kammala ziyarar tasane ya bada rahoton cewa ana buqatar kafa Hukumar "West African Examination Council",


  Bayan Amincewar gwamnatocin, Kasashen sai aka kafa Hukumar Jarrabawar ta "West African Examination council"


    Inda aka fara gudanar da jarrabawar a Wasu daga cikin Kasashe, kamar haka:-

•Najeriya

•Ghana

• Sierra Leone

 •Da kuma kasar Gambia,

      Anfara Gudanar da jarrabawarne a watan Disambar Shekarar 1951.



   A Wannan shekarar Kasar Laberiya takasa cika sharuddan da'aka gindaya, inda hakan yakawo tasgaro a gudanar da jarrabawar a Kasar, inda sai a Shekarar 1974 aka fara gudanar da jarrabawar a Kasar ta Laberiya .




   • TARON HUKUMAR NA FARKO
 
Bayan kafa Hukumar , an kira taro na farko a Accra, Babban Birnin Kasar Ghana a watan March na Shekarar 1953,


    Wanda a taronne aka kafa kwamitoci guda 5, don su dinga taimaka wa Hukumar.



Kwamitocin da aka kafa  sune:-


1.Administrative and Finance Committee

2.School Examinations Committee

3. Public Service Examinations Committee

4.The Professional, Technical and Commercial Examinations Committee

5.Local Committee.


Mutane 26 ne suka halarci wannan taron  na farko da aka gudanar a Kasar Ghana.


    Ga sunayensu:-


1.Mr. A. N Galsworthy (Shugaban Hukumar)

2. George Barker Jeffery(Chief Secretary of the West African Inter-Territorial Secretariat)

3.Mr. J. L. Brereton (Secretary of the Cambridge Syndicate)

4. membobi 13 da gomnatocin Najeriya, Ghana, Sierra Leone, da Gambia, suka zaba.

5.Sai mutane 10 daga kasashen turai.

   BIKIN CIKAR HUKUMAR SHEKARU 50 DA KAFUWA:-


   A shekarar 2002 ne, Hukumar ta WAEC Tayi bikin cika shekaru hamsin (50th anniversary) da kafuwa, Wanda aka gudanar da Bikin a Abuja, Babban Birnin Kasar  Najeriya,


   Inda Aka sanyawa taron suna "WAEC: 50 years of Excellence".

  
    Dukkan membobin kasashen West Africa sun Halarci bikin a Abuja.

  A Lokacin bikin ne aka kaddamar da Littafin
"The West African Examinations Council (1952-2002): Half a century of Commitment to Excellence and Regional Cooperation".


    Dafatan kun Amfana da wannan Tarihi na Hukumar WAEC.



      Nagode


Naku A ko da yaushe: Miftahu Ahmad Panda.


   Muna fatan zaku kasance tare da wannan shafi domin samun Sahihan Bayanai akan Harkokin Ilimi dakuma sauran Muhimman Batutuwa.



RUBUTU MAI ALAKA :


Tarihin Hukumar Jamb




Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak