Skip to main content

Abubuwan Da Yakamata Kasani Gameda Jamb Regularization




Lokacin Da kaje/Kika Je, JAMB CBT CENTER Aka ambaci Regularzation Sai kuji Wani sabon Al'amarin Da Baku sanshi ba, Kokuma Baku Da Cikakken Bayani Akan sa.

--JAMB REGURLARIZATION; tsari ne Na samar Da Admission Ga Wanda Hukumar, JAMB Bata basu Admission ba, a Lokacin Dasuka samu Admission Na Makarantar Su(Banda Na JAMB)

Eh Admission Na Makarantar su, Misali Jami'a, Kokuma NCE Ko Diploma.

 

 

Karanta : Bayani Gameda Scholarship Tareda Yadda ake nemansa

---MEYASA HAKAN?

•Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire (JAMB) a Dokar ilimi ta Kasa itace take Da Hurumin tantancewar Farko Sannan ta Baka admission Kafin Makarantar ka.

a Farko-Farkon Lamari Dalibai Sun kwana Da tsammanin Cewar Jami'a Ce Kadai Ake Shiga da JAMB kafin daga Bisani, suka Fara Sanin Mafi Yawa Daga Cikin Makarantun gaba da Sikandire, Baza su baka admission ba, Sai KAYI JAMB.

Wannan Dokar Hukumar JAMB takara karfa fa ta Ne a 'Yan Shekarun Nan.

Wannan Shine Dalilin Da Makarantun gaba da Sikandire Dayawa Suka Soke Tsarin Pre-ND a Diploma Dakuma pre-nce, a NCE, Sakamakon ko daka Kayi daya daga Cikin Su, Har Ila yau Ana Buqatar Ka sake Rubuta Jarrabawar JAMB kafin Makarantar ta baka Admission, Bayan hukumar JAMB ta baka.

Kamar yanda Nafadi a Yanzu Hukumar JAMB tana Cigaba da kalacin Dukkannin Sauran Makarantun gaba da Sikandire, Kan Suma subi wannan tsarin Na Cewar Makaranta bazata fara bada admission ba, har sai Dalibi yafara samun Admission DAGA JAMB.

a Karon Farko Dokar Tafi Tsanani ne Akan NCE, Polytechnic Dakuma Jami'o'i, Amma daga Bisani Hukumar JAMB ta shigar Da tsarin Zuwa Wasu Makarantun Monotechnics, Ma'ana kebantattun Makarantu a wani Bangare Guda Daya, kamar irin su kwalejin Aikin Noma(College of agriculture) Da kwalejin koyon Aikin shari'a(Legal)
a Yanzu Za'a Iya cewa tsarin JAMB kafin Admission, ya Kara de kowanne Bangare Da sashi Na Makarantun gaba da Sikandire, a Fadin Nigeria, in Banda school of Nursing, Kokuma College Of health Da wasu Yan Kadan.

 

 

Karanta : Abubuwan da yakamata kasani Gameda DE

---Menene Amfanin JAMB REGURLARIZATION?

Amfanin Sa ya kasu Bangare Biyu Ga Wanda Yayi diploma da Wanda Yayi Jami'a.

Wanda Yayi Diploma; Dalibin da yayi Diploma, Ko NCE Wanda a Lokacin Hukumar JAMB Bata Bashi Admission ba, Kokuma Ma beyi jamb din ba a shekarar, to a Lokacin Dayake, bukatar Shiga Jami'a, ta Hanyar Direct Entry, Dole sai yayi REGURLARIZATION, domin Hukumar JAMB tafara Bashi  JAMB Number.

Dalibin Da Yayi Jami'a; Zai Yuwu Ace Dalibi ya kammala Jami'a batare da Hukumar JAMB ta Bashi Admission ba, Sai de Dalibi Bazai samu halartar Yiwa kasa Hidima ba(NYSC) Har sai Yayi JAMB REGURLARIZATION.

Hukumar JAMB itace take Amincewa da Cewar ka, kammala Jami'a Kuma zaka iya yin Hidimar kasa ko A'a.

JAMB REGURLARIZATION a takaice; Yana Nufin wani tsari ne Na Hukumar JAMB, da takeso dole tasan Dukkan Daliban Dasuke karatu a Makarantun gaba da Sikandire, domin ta a Dana Bayanan Su (Matriculation List)
a Wannan Shekarar hukumar JAMB ta Kara Gargadin Makarantu da Kada Su Kara Bawa, Wani Dalibi Admission ba tare Da hukumar tafara Bashi ba.

Kusani Dalibai babu wani Admission, halatacce inde Sunan ka, baya cikin Matriculation List Na JAMB.

Mai karatu Zai Ce to Yaya batun Masu Part time fa, Kokuma karatu daga gida (Distance learning)

Sai Nabaka Amsar Cewa dukan su hukumar JAMB ce take fara basu Admission, domin akwai Nasu tsarin Na Daban, Wanda ya hada hadda Daliban Dasukayi Jami'a a Wasu kasashen(ABROAD STUDY) Dakuma Masu Part Time ko affiliate program.

Karanta : Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100

 
NB: Dalibai Musani Cewa JAMB REGURLARIZATION Bashi bane Change of Admission Letter.

Zaku Iya fada Mana Wasu abubuwan Dasuka Shige Muku Duhu, Domin Yin Bayani Akai.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak