Skip to main content

Madannai 9 da zaka iya amfani dasu a madadin Mouse lokacin Jarrabawar Jamb





Tun bayan mayar da jarrabawar Jamb a Na'ura Mai kwakwalwa, Hakika Dalibai da dama kan fuskanci Kalubale a lokacin gudanar da jarrabawarsu ta Jamb, sakamakon karancin Ilimin Na'ura mai kwakwalwa,wasu Dalibanma kan Gaza gudanar da jarrabawar tasu sakamakon wannan matsala, Hakanne yasa Hukumar ta Jamb ta baiwa Dalibai damar yin amfani da wasu madannai Guda 9 a madadin yin amfani da mouse, saboda wasu daga cikin Daliban kan kasa yin amfani dashi.

Karanta : Tarihin Hukumar Waec

Madannan Guda 9 Sune;

1. A- zaka Iya danna Mabullin A a cikin Keyboard dinka, idan kanason ka zabi amsar A, basai ka jawo Cursor dinka ka kaishi kan A dinba, kawai da zarar ka danna A, zai zabar maka amsar A

2. B - Idan amsar ka B ce, kawai sai kadanna Madannin B, batare da kayi amfani da mouse ba

3. C - idan kuwa amsar ka C ce to sai kadanna Mabullin C kawai, domin zabar C

4. D - Idan kuwa yakasance D ne amsarka to sai kadanna D a cikin Keyboard dinka, zai zabar maka zabi na Hudu wato D

5. P – Idan kuwa so kake ka koma tambaya ta baya, kawai ka danna Mabullin P zai kaika tambayar baya, ma'ana tambayar da ka wuce

6. N – Idan kuwa so kake ka tafi tambaya ta Gaba, Abin da zakayi kawai shine Danna Mabullin N zaka tsinci kanka a tambaya ta Gaba

7. S – Bayan ka kammala jarrabawarka, Idan kanason kayi submitting, ma'ana ka turawa Hukumar Jamb Jarrabawar ka, kawai sai kadanna Mabullin S

8. R – Idan kuwa da danna Mabullin S a bisa Kuskure, to abin da zakayi shine Danna mabullin R domin mayar dakai inda zakaci gaba da gudanar da jarrabawarka

9. Y - Idan kuwa ba abisa kuskure kadanna Mabullin S dinba, ma'ana idan so kake kayi submitting din Jarrabawar taka, to da akwai bukatar kadanna Mabullin Y bayan kadanna Mabullin S din, domin kuwa Jarrabawar taka bazatayi Submitting ba koda kadanna Mabullin S, matukar baka danna Mabullin Y ba.


Karanta : Tarihin Hukumar Nbais


  Wadannan madannai da muka lissafo, sune madannai 9 da Hukumar Jamb ta baiwa Dalibai damar yin amfani dasu a madadin Mouse.


     Yanada kyau kayi Sauri sosai a lokacin da kake gudanar da Jarrabawar ka ta Jamb, domin kuwa Ana bukatar ka amsa dukkanin tambayoyin da za'ayi maka guda 180, a cikin mintuna 120 (Awa Biyu)



    Kada kawuce Second 40 a kowacce tambaya, saboda baka da lokacin Bata Lokaci.


         
       Mungode



Marubuci: Miftahu Ahmad Panda


RUBUTU MAI ALAKA :

Tarihin Hukumar Jamb

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak