Skip to main content

Cikakken Bayani Gameda Inter-University Transfer (IUT)

 

 

 


 

 

• Me ake nufi da Inter-University Transfer (IUT)

•Kowace Jami'a ne take karbar Transfer din ?

• Yaya ake yin Transfer din ?

• Menene requirements ?

__________________________________________________________________________

•Me ake nufi da Interuniversity transfer (IUT) ?

Interuniversity transfer wani sabon tsari ne da Jami'o'in Nigeria suka bullo dashi, wanda bai zama gama gari ba, Jami'o'i kalilan ne suka dauki wannan tsari.

Karanta :Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

 
Inter university transfer wani hanya ne da yake baiwa dalibi damar canja makarantar da yake karatun degree zuwa wata Makarantar ta daban dan Cigaba da karatun shi sakamakon wasu dalilai.
Kamar Misali: Mutum yana Karatu a Yusuf Maitama Sule University sai yayi Transfer ya koma Bayero University, Kano.

• Kowace Jami'a ne take karbar Transfer din ?

A'a ba kowace Jami'a bane take karba sakamakon wannan wani sabon tsari ne da ba kowace Jami'ar bane tayi adopting dinshi.

Ga Sunayen wasu daga cikin Jami'o'in da suke karba:

1• University Of Ibadan (UI)

2• Obafemi Awolawo University, Ile-ife (OAU)

3• Kaduna State University (KASU)

4• Federal University Of Technology, Akure (FUTA)

5• University Of Ilorin (UNILORIN)

6• University Of Nigeria, NSUKKA (UN)

7• Ladoke Akintola University Of
Technology, Ogbmoso (LAUTECH)

8• Osun State University (UNIOSUN )

9• University Of Abuja (UniAbuja)

10• Ahmadu Bello University (ABU ZARIA)

11• University Of Lagos (UNILAG)

12•  Umaru Musa Yar’Adua University (UMYU)

13• Bayero University, Kano

14• Mafi yawan cin Private Universities (Jami'o'i Masu zaman Kansu)

• Yaya ake yin Transfer din ?

Akwai abubuwa Kamar guda uku da ya kamata kayi dan yin wannan transfer din, gasu Kamar haka:

 

Karanta : Yadda Ake Tattara Bayanai

1• Katattauna da Admission Officer na Jami'ar da kake so ka koma, domin ka samu tabbaci akan shin idan ka baro taka University din to su zasu amshe ka ? Idan sun tabbatar maka zasu amsheka sai ka tafi mataki na biyu, Shine:

2• Ka tattauna da admission officer din Jami'ar da kake karatu a wannan Lokacin dan kaji shin su zasu yarda su baka transfer din, domin kuwa idan basu gamsu da dalilan ka nayin transfer din ba zasu iya hana ka

3• Daganan kuma sai ka karbi form na transfer din ka cika anan Makarantar da zaka bari, sannan kuma ka cika na Makarantar da zaka koma.

Idan baka tabbatar da yarjejeniya tsakanin wadannan makarantun ba (Wacce zaka bari da wacce zaka koma) to zaka iya yin biyu babu.

•Menene Requirements

Kusan duka requirements din iri daya ne, in banda wurin CGPA kawai.

 

Karanta : Ma'anar Deferrel Tareda Amfaninsa Ga Dalibai

1• Ana bukatar transcript dinka

2• Sannan ya zama Course dinda ka baro a can anan ma shi zaka karanta. (Duk da zaka iya canjawa, amma idan kanada requirements na inda kake son canjawa din)

3• Ka tabbatar maki dinka na Jamb yakai adadin maki dinda Makarantar take bukata, sannan ka tabbatar maki din kuma yakai adadin wanda Department din suke bukata.

4• Sannan idan Makarantar ta amshe ka to aji biyu zata sanya ka, koda kuwa

5• Sannan dole ya zama kana Level 2 ne, idan ka kai level 3 to transfer din ba zai yuwu ba (Amma sai idan Course din naka mai Shekara 4 ne)

6• Zaka iya yin transfer din koda kana aji uku ne Level 3, idan course dinka mai Shekara 5 ko 6 ne.

Amma dai Mafi kyau shine ka tuntubi hukumar gudanarwa ta Jami'ar.

 

Rubutuka Masu Alaka :

  Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100

 Bayani Gameda Scholarship Tareda Yadda Ake Nemansa

 Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda Jamb Regularization

Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda DE 

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak