Skip to main content

Ma'anar Deferral Tareda Amfaninsa Ga Dalibai





•°••°•Kafara Karatun ka Kwatsam Sai Wani Dalili Yatilasta Maka Dole Sai Ka Dakatar Dashi Zuwa Wani Lokacin...

•Ma’anar Deferring
•Amfanin Sa
•Lokacin Yinsa
•Yanda akeyin Sa:

•√Deferring Yana Nufin Neman izinin Dakatar Karatun ka Daga Wata Makarantar Gaba Da Sikandire Data Baka Admission, Kafin Fara Karatu ko bayan Farawa, Dakatarwar Tana kasancewa ne Ta Shekara Daya Galibi, Kuma Bisa Wani Babban Dalili.

Karanta :Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

 
Misali Sakamakon Wahalar Samun Admission Kokuma Kudaden Da ake Kashewa Dakuma Hanyoyin Da'ake Bi Kafin Samun admission, bayan samun Admission Din, sai Kuma Wata Babbar Matsalar ta tasowa Dalibi da tasa Dole baze iya yin Wannan Karatun ba a Wannan shekarar to zai aikawa Makarantar databashi Admission din wasiqar Neman Amincewar ta zai Dakatar Da Karatun Na Tsawon Shekara Daya.

•√Amfanin Deferring Ga Dalibi; Amfanin sa Shine Adana Gurbin Karatun sa a Lokacin da Barin sa Yazama wajibi bisa Wasu Dalilai Misali:
Rashin Kudin Gudanar wa na Makaranta,
Rashin Lafiya
Ko Rasuwar Wani Makusanci da rashin sa Yayi Matuqar Shafar Rayuwar Dalibi, kode Wani Dalili Karbabbe.

Saide  Ba'a Kowanne Depertment Bane Hukumomin Makarantu Suke amincewa Da Deferring Mafi Yawanci Hukumomin Makarantun basa amincewa da Deferring din a Courses irin Su Medicine da Wasu Manyan Courses Da'ake ganin be Dace ba a bar Gurbin Karatun Dalibin da har Wani Dalili yasa sai ya Dakatar Da Karatun sa.

•√Lokacin Da'ake Deferring; yadanganta Da Makaranta ne Wata Makarantar tana amincewa Da Deferring Koda Dalibi Bai Fara Karatu ba Matuqar yasamu Admission Kuma Yayi Rijista, Yayinda Wata Kuma Dole sai Dalibin Yafara Karatu a Makarantar Kuma a qalla Hukumar Makaranta taduba Sakamakon Jarrabawar sa taga Yanada kokari.

Karanta : Bayani Gameda Scholarship Tareda Yadda Ake Nemansa

•√Yanda make Deferring; Bayan Dalibi Ya Yanke Shawarar Dakatar Da Karatun sa, Zai Rubuta Wasiqar Neman izinin Dakatar Da Karatun ne (Deferral Letter)  Cikin Wasiqar Dalibi Zai  Rubuta Dalilin sa, na Yin Deferring Din, Zuwa Ga  Ofishin Admission Officer Kokuma Registerer Na Makarantar sa Bayan Amincewar Admission Officer Kuma sai Dalibi Ya Sanar Da HOD Da Deen Na Depertment dinsa Suma a Rubuce tare Da shedar amincewar Hukumar Makaranta.

•°•Abubuwan Lura:

•Dalibi Yayi Shawara Da iyayen Sa

•Ya tabbatar Dalilin Nasa Na Gaskiya ne Kuma Hakan shine Mafita ga Rayuwar sa

•Ya Tabbatar Ya Rubuta Dalilin Nasa Na Gaskiya Kar Yaboye

•Ya Tabbatar Yabi Qa’idar Da Makarantar sa ta gindaya

•Kada Deferring Din Yawuce Shekara Daya(Wasu Makarantun Suna qayyade Shekara Daya Ne).

 

Karanta : Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda DE

@ASOF. 2021
WHATSAPP>08038485677.


Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta NECO

    Biyo bayan Sakin Sakamakon Jarrabawar NECO da Hukumar Shirya Jarrabawar tayi Shiyasa wannan Shafi Na Pandancy yaga Dacewar Yayi Rubutun da Zai nunawa Dalibai Hanyar da Yakamata Subi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu Cikin Sauki batareda shan wasu Wahalhalu ba,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar taka ta NECO sune :   Karanta : Tarihin Hukumar Jamb •> Da farko kashiga Browser din wayarka Sai Kadanna Gurin Bincike (Search) Sai karubuta Adireshin result.neco.gov.ng, Sai kadanna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken •> Bayan Shafin Yabude Zai Baku wasu Akwatina Guda Hudu, Akwati ta Farko An Rubuta Exam Year, Abinda Ake Bukatar kasanya a cikin wannan Akwati shine Shekarar da karubuta Jarrabawar taka ta NECO Misali 2020, ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zakuga An rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shine wacce Irin Jarrabawa kakeson Dubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External Novemb...