Skip to main content

Bayani Gameda Two Sittings Tareda Yadda Ake Amfani Dashi





•Menene Two Sittings ?



     Two Sittings a Bangaren Ilimin Najeriya Yana nufin yin Amfani da Jarrabawoyin Kammala Makarantar Sakandire Guda Biyu, da Akayisu a Lokuta Daban-Daban, a Wasu Lokutanma daga Hukumomi Daban-Daban, Wadanda Kasamu Nasara a Wani Fannin a Jarrabawa ta Farko, kuma ka ƙara Samun Nasara a Wasu Fannonin a Jarrabawarka ta Biyu, Wadanne idan Kahada Jarrabawoyi Biyun Zasu Samar maka da Abinda Makarantu Suke Bukata Domin baka Gurbin Karatu ko Kuma Halartar tantancewa.


Karanta : Ma'anar Deferrel Tareda Amfaninsa


  •Menene Yake Sanyawa Ayi Amfani da Two Sittings ?



    Ana Amfani da Two Sittings ne idan Yakasance bakaci Dukkannin Darussan da Ake Bukata Domin Baka Gurbin Karatu a Jarrabawa Dayaba, Kuma Sai Yakasance kanada Ragowar Abubuwan da Ake Bukata a Daya Jarrabawar taka, Misali Wajibine Sai Kaci English da Mathematics a Jarrabawarka Kafin a Baka Admission a Jami'o'in Najeriya, to Idan Yakasance Jarrabawoyi Guda Biyu kayi, Misali Kayi NECO da WAEC, Kuma Kasamu English a Neco Amman Bakada Mathematics, kuma Kasamu Mathematics a WAEC dinka Amman Bakada English, to a Irin Wannan Yanayin Zaka Iya Hada Jarrabawoyin Guda Biyu kayi Amfani dasu domin Neman Gurbin Karatu.


Karanta Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta WAEC a Sakon Message


  •Shin Dukkannin Manyan Makarantun Najeriya Suna Karbar Two Sittings ?



   Kwarai da Gaske, A  yanzu mafi yawa, koma ince Dukkannin Manyan Makarantu da Jami'o'in Najeriya Suna Karbar Two Sittings Domin Bada Gurbin Karatu, Saidai Amman Akan Samu Banbanci Akan Irin Jarrabawoyin da Makarantun Sukan Amince su Karba a Matsayin Two Sittings din.


  •Shin Wadanne Jarrabawoyi Makarantun Najeriya Suke Karba a Matsayin Two Sittings ?


    Hakika Mafi Yawancin Makarantun Najeriya suna Karbar Jarrabawoyi Daban-Daban a Matsayin Two Sittings Misali : Dukkannin Manyan Makarantun Kasarnan suna Karbar Jarrabawar NECO da Wata NECO din da Aka hadasu a Matsayin Two Sitting, koda Kuwa Anyisu A Shekaru Daban-Daban ne, kuma Koda Sun Kasance Jarrabawoyin SSCE da GCE ne, Haka Zalika Makarantun na Najeriya suna Karbar Hadakar Jarrabawoyin NECO da WAEC a Matsayin Two Sittings, Sai dai kuma wasu Makarantun Basa Karbar Hadakar Jarrabawoyin NECO da NBAIS, Ko NECO da NABTEB, Ko WAEC da NBAIS ko WAEC da NABTEB a Matsayin Two Sittings, Amman Mafi Yawancinsu suna Karbar Jarrabawoyin NBAIS da NABTEB suma a Matsayin Two Sitting.

KarantaBayani Gameda Scholarship Tareda Yadda Ake Nemansa


      Shin Wannan Rubutun Ya Ƙayatar daku ?.



   Kusanar damu ta Comment Box domin Kara Mana Karfin Gwuiwa, Haka Zalika Kunada Damar Sanar damu Idan Akwai Wani Bangare da Kuke Bukatar Muyi Muku Rubutu Akansa.




      Kada Kumanta Kusanar da Abokai da Ƙawayenku Domin Su ma Suzo su Karanta su Amfana.




      Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy.




Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak