Dalibai da Dama Sukan Rasa Admission, a Yayinda Wasu kuma Sukan Sha Wahala Matuka Bayan sun Samu Gurbin Karatu, Sanadiyyar Kura-Kuran da Akan Samu a Bayanansu na Shafin Hukumar Jamb wadanda basusan da Suba, Kuma Akan Samu Kuskuren ne daga CBT Centres tun daga Lokacin Yiwa Daliban Rijistar Jamb, Hakanne Yasanya muke Shawartar Dalibai da Su dinga Sanya Lura Matuka a Lokacin da Ake Shigar da Bayanansu a Manhajar Jamb (Jamb Portal),
Bugu da Kari Yanada kyau Dalibai su dinga Daukar Matakin Bincikar Bayanan nasu da Aka Sanya Musu a Shafin Hukumar Jamb Domin Fahimtar ko sunada Gyararrakin da Suke Bukatar Gyarawa a Bayanansu kafin Lokaci Yakure musu,
Hakika Matakan Bincikar Bayananka dake Shafin Hukumar Jamb ba wani Abune Mai Wahala ba, kuma Matakan Aiwatar da Hakan Suma Basuda Wahala Sam-sam, Domin kuwa Suna Kamanceceniya da Rubutunmu da Mukayi a Baya, Akan Yadda Zaka Canja Password Dinka na Shafin Hukumar Jamb , Duk da dai daga Karshe Matakan Sun Banbanta,
Ga Yadda Zakayi Domin Ganin Bayanan naka👇:
Karanta : Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawarka ta NECO na Token Code
• Abu na farko da Zakayi Shine Kabude Browser din Wayarka Sai Kashiga Shafin Login na Hukumar Jamb tahanyar Sanya Adireshin Jamb.org.ng/efacility/, Bayan Kasanya Wannan Adireshin Sai Kadanna Mabullin Search,
• Bayan Yabude Kai tsaye Shafin Zai baka Wasu Akwatuna Guda Biyu, Akwati ta Farko An Rubuta Email Address, to Ana Bukatar kasanya Adireshin Email din da Akayi maka Rijistar Jamb dashi, Sai kuma Akwati ta Biyu da Aka Rubuta Password, Abinda Ake Bukatar Kasanya a wannan Akwati sune Lambobinka na Sirri (Wanda a Mafi Yawan lokuta basa Wuce 123456) Amman koda Basu bane to Password dinka dai Ake Bukatar kasanya a Gurbin, Bayan Kasanya Wadannan Bayanai sai Kadanna Mabullin Login dake ƙasan Akwatunan,
• Bayan Shafin naka Yabude daga Sama zakaga Yana Yimaka Lale Marhaba, kuma Zakaga Sunanka tareda Profile Code din da Kabude Profile dashi, daga Kasansu kuma Zakaga Wani Mabulli da Aka Rubuta My Profile sai Katabashi,
•Bayan Yabude Zakaga Sunanka daga Sama, daga Bangaren Hannunka na Dama Kuma Zakaga An Rubuta My Documents Cikin Jar Kala, Sai kuma Daga Bangaren Hannunka na Hagu Zakaga An rubuta Change Password Cikin Koriyar Kala,
Karanta : Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta Neco
• Daga Kasan Wadannan Alamomi Kuma Zakaga An Rubuta Personal Information, to Sai Kajawo Gurin, Inda Ananne Zakaga Dukkannin Bayananka da Suke Shafin Hukumar, Kamar Sunanka, Lambar Wayarka, Jihar ka, Karamar Hukumarka, Shekarar Haihuwarka, da sauransu, Kamar Yadda kuke Gani a Wannan Hoton dake Kasa :
• Bayan Kaduba Wadannan Bayanai naka, Idan Akwai Bayanin da ba'a saka maka Daidaiba, Zaka Iya Zuwa Kayi Data Correction (Green Card), Domin Gyara Maka Kura-Kuran dake Ciki.
Ku Danna nan Domin Kallon Wannan Darasi Cikin Hoto Mai Motsi na Video a Tashar mu ta Pandancy TV, Kuma Kada Kumanta Ku danna Mana Subscribe,
Karanta : Abubuwan da Yakamata Kasani Gameda DE
Shin Wannan Rubutun Ya Amfaneka ?, Sanar damu ta Comment Box Domin ƙara mana ƙarfin Gwuiwa, Kuma kada Kamanta Kasanar da Abokanka Domin Suma Suzo Su karanta,
Mungode da Ziyartar Shafin mu Mai Farin Jini na Pandancy
Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.
Rubutuka Masu Alaka :
Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu Lokacin Jarrabawar Jamb
Yadda Zaka Gane idan Anyi Maka Uploading din O'level Result dinka a Portal din Jamb
Yadda Zaka Duba tareda Karbar Admission dinka a Portal din Jamb
Comments
Post a Comment