Skip to main content

NYSC : Cikakken Bayani Gameda Banbancin Remobilization da kuma Revalidation

 




National Youth Service Corps (NYSC)


• Remobilisation ba na kowa da kowa bane


•Bambancin REMOBILIZATION da kuma REVALIDATION

______________________________________________________________________


•Remobilisation ba na Kowa da Kowa bane


Hukumar gudanarwa ta dalibai masu yima kasa hidima (Bautar Kasa) ta fitar da Sanarwa akan Remobilisation inda take bada sanarwar cewa idan lokacin da ta bada da farko ya cika ba zata kara wani ba.

Saidai miliyoyin tambayar da dalibai sukeyi shine kowa ne zaiyi Remobilisation din ? A'a ba kowa bane sai wanda yake a Batch B (NYSC 2020 BATCH B).

Karanta : Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

•Me ake nufi da Remobilisation ?


A karkashin wannan rubutun zaka fahimci abinda ake nufi da REMOBILISATION kai har ma da REVALIDATION.


REMOBILISATION wani terms ne na masu yiwa kasa hidima da suke amfani dashi.


REMOBILISATION wani tsari ne da yake bawa dalibin da zaiyi wa kasa hidima damar sabunta Program dinsa na yiwa kasa hidimar, sannan ya Cigaba daga inda ya tsaya.


•To Su waye suke da damar yin REMOBILISATION din ?


Wadanda suke da damar yin REMOBILISATION sune wadanda sukayi Online registration na tafiya Bautar kasa din, lokacin da aka fara, kuma har sun tafi Camp sun fara komai da komai amma daga baya sai wani matsala ya hanasu Cigaba da zama q Camp din.

To wadannan sune wadanda zasuyi applying (nema) REMOBILISATION aduk lokacin da hukumar ta bada damar hakan domin suje su karasa program din nasu.


•Misali:


Mr. A ne yayi Online registration na NYSC yabi duk wasu Process har ya zama an tura shi Camp, bayan ya fara da kamar Sati daya sai wani dalili (Kamar rashin lafiya) ya hana shi karasa zaman Camp din, dan haka ya koma gida, to yanzu yaji sauki dan haka zai koma ya karasa Camp din nashi, to sai yayi REMOBILISATION.

Karanta : Ma'anar Deferrel tareda Amfaninsa Ga Dalibai

•Me ake nufi da REVALIDATION ?


REVALIDATION shima kamar REMOBILISATION ne ta bangaren wanda zaiyi shi, domin ba fresh Candidate bane yake yi, a'a wanda daman ya Riga yayi ne.


REVALIDATION wani tsari ko hanya ne da yake bawa dalibin da zai yiwa kasa hidima damar Sabunta Online Registration na NYSC din sa da daman ya Riga yayi.


•Wane Coper ne yake da damar yin REVALIDATION ?


Gungun daliban da suke da wannan damar sune: wadanda daman sun riga sunyi registration din su na NYSC lafiya lau, amma sai suka ki zuwa suyi reporting a Orientation Camp saboda wasu dalilai ko kuma haka kawai ba tare da wani dalili ba, to wadannan sune zasu yi REVALIDATION.


Misali:

Mr. B ne yayi Online registration na NYSC din sa, sai aka tura shi Bayelsa acan zaiyi Camp to amma sai yaki zuwa yayi reporting a Bayelsa din har lokacin ya wuce ko da karbabben dalili ko ba dashi ba, to anan ana bukatar Mr. B yaje yayi REVALIDATION.


Saidai fa Shi REVALIDATION ba kamar REMOBILISATION bane, shi REVALIDATION ana yin sa ne by Batch amma ba by Stream ba.

Idan kayi missing bakayi reporting zuwa Camp din ba a wannan Stream din a wannan Batch din, to ba zaka iya yin Revalidation din ba a wani stream, sai dai kuma ka jira wani Batch din.

Amma kar ka damu, domin kuwa idan har Corp member bai tafi Camp din ba a Stream din da ya kamata ya tafi ba, to kai tsaye an cire shi daga wannan Stream din an kaishi na gaba, dan haka babu maganar REVALIDATION kenan, Amma idan ya zama wannan Stream din shine na karshe a wannan Batch din to ba za'a daukeshi kai tsaye akaishi a wani Batch ba dole sai yayi Revalidation.


Misali:

Mr. C ne zai tafi Service a Stream i, to amma sai bai tafi ba, to anan ba zaiyi REVALIDATION ba, kai tsaye (Automatically) an mayar dashi Stream ii.

Amma idan Mr. D zai tafi Service a Stream ii sai bai tafi ba, kuma Stream ii dinnan shine karshe a wannan Batch din, daga wannan sai wani Batch kuma, to anan dole sai Mr. D yaje yayi REVALIDATION.

Karanta : Cikakken Bayani Gameda Inter-Faculty Transfer (IFT)

Bissalam

ASOF_2021

12/02/2021

Arewastf@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith. > A

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba b

[Shin Ko Kasan] Kasashe Nawane A Duniya ?

Ganin Muhimmancin Sanin Adadin Kasashen da suke Duniya Ga Al'umma yasa Shafin Pandancy yayi nazari tareda Binciko muku Adadin Kasashen da suke a fadin Nahiyoyin Duniya Guda  6. Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu    Hakika a yanzu haka da akwai Kasashe Guda 195 a Duniya,    Ga yanda Lissafin yake👇 > Nahiyar Afirka itace Nahiyar da tafi kowacce Nahiya Yawan Kasashe a Duniya inda take da Kasashe Guda 54 > Sai kuma Nahiyar Asia da take da Kasashe 48 a matsayin Nahiya Ta Biyu > Sai kuma Yankin Turai wato Europe wadda take Dauke da Kasashe Guda 44 >  Sannan sai Bangaren Latin America wadda suke da Kasashe Guda 33 > Sai kuma Oceania masu Kasashe 14 > Sai kuma Bangaren Arewacin Amurka wato Northern America wadda take da Kasashe 2 kacal.     Mai karatu Idan Ka tattara jimillar Adadin wadancan Kasashe zasu baka Adadin Kasashe 195 wadda sune Kasashen da muke dasu a Fadin Duniya a halin yanzu Karanta : Yadda Zak