Skip to main content

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code




   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,

    Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :
 
Karanta :Tarihin Hukumar NECO

•> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng,

•>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi,

•> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi Wadannan Lambobi baka taba siyaba ba wannan Gurin zaka Dannaba, Abinda Zakayi shine katafi Daga Kasan Shafin Inda Zakaga an rubuta  Don't Have An Account ? Register here, da koren Rubutu sai katabashi,

•> Bayan Yabude Zai baka wasu Akwatuna Guda Biyar, Akwati ta Farko itace Full Name ; Ana Bukatar Kasanya Cikakken Sunanka a Cikin wannan Akwatin, Misali; Miftahu Ahmad Panda

ii. A cikin kwati ta Biyu kuma Zakaga An rubuta; Phone Number, Abinda Ake Bukatar kasaka a Cikin wannan Akwatin itace cikakkiyar Lambar Wayarka, Misali; 08039411956,

iii. Sai kuma Akwati ta Uku Wacce Zakaga An rubuta Email Address: Abinda Ake Bukatar kasaka a wannan Akwati shine Adireshinka Na Email, Misali;  miftahuahmadpanda@gmail.com,

iv. Sai kuma Akwati ta Hudu Wacce Zakaga an rubuta Password, Abinda Ake Bukatar kasanya a wannan Akwatin sune Lambobi ko Kalmar Sirrinka, Misali; 123456,

v. Sai kuma Akwati ta Karshe wacce Zakaga An rubuta Confirm Password, Ana Bukatar ka kara Sanya Kalmar Sirrinka a Cikin wannan Akwatin, Daganan Sai Kadanna Mabullin REGISTER da Zakaga an rubuta a kasan Wadannan Akwatunan a Zagaye da Kore.

   Bayan Kadanna Wannan Mabulli to shikenan kayi rijista, Abu nagaba da Zakayi shine kasayi Lambobinka Na Token Code,
 
Karanta : Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta WAEC a Sakon Message

•>Bayan ka koma Shafin da zaka sayi Lambobin Token Code din Zakaga wasu Akwatuna guda Biyu, Akwati Ta Farko an rubuta Email Address, Akwati ta Biyu kuma an rubuta Password, Sai kasanya Email Address tareda Password din da kayi rijista dashi, Sai kadanna Mabullin Login da Zakagani A Zagaye da Kore a Kasan Akwatunan Guda Biyu,

•> Bayan Yabude Sai Kadanna Mabullin PURCHASE TOKEN,

•> Daganan Sai kazabi Lambobin Token din da kakeson kasaya, sai kuma Kadanna Mabullin PAY NOW,

•> Daganan Zakaga Hoton Receipt dinka Yabayyana a Fuskar sai kuma kadanna Mabullin PROCEED TO PAY, Domin Biyan kudin Token Code din naka.


   Bayan kabiya Kudin, to shikenan kasayi lambobinka Na Token.

   Daganan kuma zaka iya zarcewa shafin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO domin Duba Sakamakon Jarrabawarka.

Karanta : Tarihin Hukumar WAEC

   
  Wannan shine Takaitaccen bayani gameda Yadda Ake Sayen Lambobin Token Code a Shafin Hukumar NECO.


   Ku Cigaba da Kasancewa da Wannan Shafi Na Pandancy domin Samun Sahihan Bayanai gameda Fannin Ilimi tareda Sauran Muhimman Fannoni, Kada Kumanta kuyi Share Domin Su ma Sauran Dalibai su Amfana.


     Nagode Sosai.


Daga Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda (08039411956).
 

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Abubuwa 10 Da Yakamata Ka tanada Kafin Lokacin Rijistarka ta Jamb

     Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.      Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,  domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka: 1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala). 2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yaf...