JAMI'A A TAFIN HANNUN KA •Jami'a wuri ne na rashin tarbiyya •Jami'a wuri ne na Kazo-nazo • Me yasa ake tsoron auren Macen da take Jami'a ________________________________________________________ •SHIMFIDA: Jami'a wani wuri ne da jama'a da dama suke ma kallon wuri na cikakken 'yancin yin abinda kaga dama (Total Freedom) ba tare da an takura maka ko matsa maka ko hana ka, ko tsangwama ba (Discrimination). Atakaice, anai mata kallon wuri ne na rashin samun cikakkiyar tarbiyya kuma wuri ne na rashin da'a (Discipline) kazalika wuri ne da yake Lalata Samari da 'yan matan da suke karatu a wannan wurin (Jami'ar) sakamakon cikakken 'yanci (Total Freedom) da ake ganin suna da shi, Wannan dalilin ya sanya dayawa daga cikin iyaye sukan hana 'ya'yan su Cigaba da karatu mai zurfi na Jami'a don gudun lalacewar tarbiyyar su, kai hatta ma samari sukan fuskanci irin wannan matsalar (Dan ko ni Mai rubutu mama na tana shan yimun Nasiha akan na kula ...