Skip to main content

Abubuwan da Yakamata Kayi Domin Samun Nasara a Jarrabawarka ko Interview





        A Yau  Rubutun Namu Zai Mayar da Hankaline Akan  Abubuwan da Yakamata kayi Domin Samun Nasara a Jarrabawarka ko Interview,


    Dafatan Zaku Biyomu, 


   Muje Zuwa 👇

Karanta : Tarihin Hukumar Jamb

  • Kayi Karatu Sosai Kuma Ka tabbatar Ka fahimci Yadda Zakayi Spelling din Kalmomin da Bakasaba dasuba


  • Ka tabbatar ka halarci Gurin Jarrabawarka Akalla Mintuna 30 Kafin Lokacin Fara Jarrabawar


  • Ka tabbatar da Cewar Ka Mallaki Abubuwan da Ake Bukata a Lokacin Zana Jarrabawar Kamar Biro da Pensir, Takarda, Ruler, Eraser da Sauran su


   • Ka tabbatar kamallaki Biro tareda Fensir fiyeda Guda Daya, Saboda Gudun ko ta kwana


   •Idan An baka Takardar dake Dauke da Tambayoyin da Zaka Amsa (Question Paper), Kayi Kokarin Karantata Anitse kuma Kaduba Adadin Tambayoyin da Zaka Amsa


   •Idan Aka Bada Damar Fara Jarrabawar, Kafara da Tambayoyin da Kasan Amsarsu kuma sukafi Yawan Maki, daga Bisani sai kahaura kan masu Kananun Maki


   • Kayi Rubutu Mai Kyau, kuma  ka tabbatar bakayi Spelling Mistake ba, kuma ka guji Yawan soke-soke, Sannan Ka tabbatar kabi Ka'idojin Rubutu a Rubutunka


   •Kaguji Surutu Ko Yawan Yiwa makobcinka magana a Dakin Jarrabawar 


   •Ka tabbatar baka Lalata takardar Jarrabawarka ko kuma Ka dukunkunata tayi dattiba


  • Idan Wani Abu Yashige Maka Duhu Ka tuntubi Invigilator, Idan an Bada Damar hakan

Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka ta Jamb a Sakon Message

   • Kada Kayanke Tsammanin Samun Nasara a Lokacin da Kake Gudanar da Jarrabawar, Ammanfa kaguji Rawar kai ko Giringidishi


   • Kadinga lura da lokaci a lokacin da Kake Amsa Tambayoyin ta Yanda bazaka cinye Dukkannin lokacinka a Amsa tambaya Dayaba


   • Ka tabbatar ka kammala Jarrabawarka a kalla Mintuna 10 Kafin Lokacin da Aka sahale muku yafita, ta Yanda zakayi Amfani da lokacin Don Sake Bibiyar Amsoshin da Ka rubuta


   •Idan Yakasance Tambayoyin da Akayi maka sunyi maka Sauki da yawa ta Yanda ka Amshesu batareda bata lokaciba, Kada Kayi Gaggawar Mika Takardar Jarrabawarka, Kasake bibiyar Amsoshin da Ka rubuta Dan Kagane ko Kayi Kuskure


   •Kabi Jarrabawarka da Addu'ar Samun Nasara, Saboda Addu'a tana Tasiri Matuka Wajen Samun Nasarar Kowacce Irin Jarrabawa.



    To Anan Zamu Dakata da Wannan Rubutu,

Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb

     Idan Rubutun Yaburgeka kuma Yakayatar da kai ka Sanar da Abokinka Shima Yazo Yakaranta,



    Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy.



     Naku a Kullum : Miftahu Ahmad Panda.


Rubutu Mai Alaka :

Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Abubuwa 10 Da Yakamata Ka tanada Kafin Lokacin Rijistarka ta Jamb

     Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.      Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,  domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka: 1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala). 2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yaf...