Skip to main content

Lokacin da Yafi Cancanta Kayi Karatu





    Ganin Yadda Dalibai da Dama sukanyi korafin cewar Sunayin Karatu iya Karfinsu Amman Karatun nasu Yakan Gaza Zama a Kwakwalwarsu, Yasanya a Yau Shafinku Mai Farin Jini na Pandancy zaiyi Muku Bayani Akan Sahihin Lokacin da Yafi Cancanta Ayi karatu Domin Fahimtar Karatun Dari bisa Dari tareda Zaunawarsa a Kwakwalwa batareda Ya rushe ko an Mantashiba,



      Sayen Littattafan Karatu abune Mai Muhimmanci Matuka a Cikin Karatu, Amman ka kasance Mai Dabi'ar Son Karatu Shima Muhimmin Abune,

Karanta : (Shin Ko Kasan) Kasashe Nawane a Duniya ?

    Hakika ba Kowanne lokacine yadace Ayi karatuba, Matukar karatu akeson Ayi na Fahimta, Misali Karfe 12 na Rana Sam-Sam ba Lokacin Karatu bane, Wajabtawa Kanka Karatu a Irin Wannan Lokacin kawai Zaisa Ka Wahalar da kankane, Amman Zai wahala kaga Karatun Yazauna, Saboda da tsakar rana lokacine da Kwakwalwa take Bukatar Hutu, Dan haka tilasta mata Akan Sai tayi Aiki Zai Zama Wahalar da Kaine Kawai,


    Sahihin Lokacin da Yafi Cancanta Ayi karatu shine : Bayan Sallar Asuba zuwa Wayewar Gari, Ko kuma da Yamma Kamar daga Karfe 4 zuwa 6 na Yamma, Babu laifi Idan Anyi Karatu da Daddare Shima Yana Zama a Kwakwalwa, Amman kada Ka takurawa kanka akan cewar sai kayi karatu matukar kanajin Barci, Idan Kana Cikin karatu Kaji Barci to kawai katafi kayi kwanciyarka, 


   Haka Zalika kada Kadinga Tsawaita Karatun naka Yakasance yayi Tsawo da Yawa, Abinda Yafi Kamata Shine Kada Kadinga Haura Awanni 3 a Lokacin da Kake Karatun, Saboda Idan Ka tsawaita Karatun to wanda kayi ma tunda fari  Shima Zai rushe, Tsawaita Awannin Yin Karatu Bashi Yakesa a Fahimci Karatuba,


    Yanada Kyau ka Shirya Jadawalin Karatunka, ta Yanda Zai Kasance Kowanne Subject ko Course akwai Lokacin da kaware Domin Yin Karatunsa, Misali Bazai yiwu ace zaka Karanta English, Mathematics, Physics da Chemistry Dukka a lokaci gudaba, Yanada Kyau ka Rarraba lokacin Karatun Kowanne Course Yakasance lokacin karatunsa daban,


Karanta :Cikakken Bayani Gameda Jami'a tareda Dalilan da Sukasa Ake Tsoron Auren Macen Datake Jami'a

     Idan Yasance da Daddare zakayi Karatu kada Kayi Amfani da Fitila Mai Hayaki, Misali Kamar Fitilar Kwai, Saboda Shigar Hayaki Cikin Idanunka Zai iya Haifarmaka da Gagarumar Matsala anan gaba,  Kayi Amfani da Ingantacciyar Fitila kuma Kazauna a Ingantacciyar Kujera ko Teburi, Kada Ka Kwanta sosai a lokacin da Kake Karatun Saboda hakan Zai janyo kaji Kanajin Barci, Sannan Kayi Karatunka a Hankali batareda kana Kwallawa da Karfi ba, Saboda zakafi Samun natsuwa idan Kana Karatunka a hankali, 


   Daga Karshe Yanada Kyau Yakasance kaci ka koshi a lokacin da Zaka fara karatu, Saboda Yunwa tana Hana Fahimtar Karatu Kwarai da Gaske.


Karanta : Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka ta Hannu

     To Yau ma Anan Zamu Dakata a wannan Rubutu Namu,


   Idan Rubutun Yakayatar daku Kusanar damu ta Comment Box, Domin Kara mana Karfin Gwuiwa, Kuma Kusanar da Abokananku Domin Suma Suzo Su Karanta.


    

    Mungode da Ziyartar Shafin Pandancy




Naku a Kullum : Miftahu Ahmad Panda.


Rubutu Mai Alaka :

Yadda Yakamata Dalibi Yayi Karatu

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Abubuwa 10 Da Yakamata Ka tanada Kafin Lokacin Rijistarka ta Jamb

     Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Hukumar Shiryawa Da Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire ta Ƙasa (Jamb) Zata iya Bayyana Ranar Fara Yin Sabuwar Rijistar JAMB, wacce Ɗalibai Suka Daɗe Suna Jiran ta.      Kowacce Shekara Hukumar Na Fitar Da Sababbin Tsare-Tsare, Tare Da Bayyana Su,  domin kaucewa da Magance Wasu Matsaloli Ga Dukkan Daliban Dasuka Shirya Yin Sabuwar Rijistar JAMB ta wannan Shekarar, Ga Abubuwan Da yakamata Ɗalibai Suyi, ko Su Tanada kamar Haka: 1•Phone Number (Wacce Kayi Rijistar ta Dakan ka) : Ana Bukatar Ɗalibi Ya Mallaki Lambar Wayar da Zaiyi Rijistar sa ta Jamb da ita Kafin Lokacin dazai garzaya domin yin Rijistar tasa, Kuma Da So Samune ma Zaifi Kyau a ce Shi yayiwa Layin Rijista (Saboda Gudun Matsala). 2•Akwatin Aika Sako na Gmail (Ba Yahoo ba, Kuma Wanda Kayi Rijista da Lambar Wayar ka) : Yanada Kyau a ce Ɗalibi Ya Mallaki Adireshinsa na E-mail, Musamman ma na Kamfanin Google wanda akafi sani da Gmail, Saboda Yaf...