Skip to main content

Abubuwan Da Yakamata Kasani Game Da DE










Cikakken bayani Akan Direct Entry (D.E)


  •Menene Direct Entry (D.E)

  Direct Entry ko D.E a takaice wata dama ce ko hanya wacce idan kabita zata kaika kowacce irin jami'a dake fadin Najeriya, Sannan kuma zaka fara karatunka ne daga Aji biyu (Level 200/ UG 2), duk da akwai wasu Departments a wasu jami'o'i wadanda su idan sun baka admission din to dole daga Aji daya zaka fara (Level 1) tare da wadanda suka shiga ta hanyar Jamb.

Hakanan kuma Direct Entry anayin Rijistar ta ne sau daya a shekara itama kamar JAMB, Sannan Kuma Mafi Yawancin Makarantun Basa Shirya Wata Jarrabawa, Akan D.E, Sai de Tantancewa ta internet(online screening) Dakuma Physical screening, Wasu Makarantun Kuma suna Shirya Jarrabawa, ko interview.

Kamar Jami'ar Bayero a Shekarar Data Gabata ta Shirya Jarrabawa Ga Daliban Dasuke Neman Makarantar, ta Hanyar D.E Amma a Faculty Daya Kadai (Allied Science) banda Sauran.

Karanta : Manyan Jami'o'in Najeriya Guda 100

---Su waye Suke da Damar Neman Jami'a ta Hanyar Direct Entry?

 •Direct Entry din (D.E) Ba kowanne dalibi yakeda damar zuwa jami'a ta hanyarsa ba, sai Wanda yakeda daya daga cikin wadannan takardun  shaidar kammala karatu, kamar haka:-

    1• Ordinary National Diploma Certificate (OND)

    2• Higher National Diploma Certificate (HND)

    3• GCE A Level, HSC, DALF Certificate

    4• Nigerian Certificate Of Education (NCE)

    5• Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN)

    6• National Diploma (ND)

    7• First Degree (Bsc, B.A, BAEd, LL.B)

    8• National Innovation Diploma (NID)

•Necessary Requirements

Sannan kuma dole sai ka cancanta ta hanyar samun:-

1• Credit Biyar a SSCE dinka, kuma kar ya wuce zama biyu (Two Sittings)

2• Mafi karanci kaci Lower credit a ND, ko NID tareda Requirement na O'level

3• Hakama Wanda yakeda 3rd Class a digiri dinshi na farko shima ana bashi



Karanta : Zamantakewar Matasa


FADAKARWA:-

Anan zaka iyayin applying Direct Entry da certificate din Digirinka na farko, Misali; kayi digirinka na farko a Law LL.B to kuma kanaso kayi wani digirin a fannin ilimin kimiyar siyasa (Political Science) to ba sai kayi Jamb ba, kawai sai kayi amfani da wannan certificate din digirin naka na law LL.B saika siya D.E form kacika shikenan zasu baka level 2.

•Post Graduate Diploma;

Sannan akwai banbanci tsakanin wannan da postgraduate diploma, ita postgraduate diploma kamar misali kagama digirinka na farko a Political Science to amma kuma kanaso kayi master's degree dinka ne a Public Administration, to madadin ace bazakayi masters dinba saikaje tukuna kayo degree, a public administration din to shine sai aka sama maka sauki cewa kaje kayo wannan postgraduate, diploma din sannan bayan ka gama saikazo kayi masters degree dinka a public administration saboda idan kun lura zakuga sunada alaka da juna sannan kuma suna faculty daya ne.

•Post Graduate Diploma a Law Da Medicine;

Amman Ba'ayin postgraduate diploma a law da medicine, sai idan degree din naka na farko kayishi ne a wani course dayake karkashin faculty of law din, kamar misali kayi Degree dinne a private law, to zaka iyayin postgraduate diploma din domin kayi Master's dinka awani law din na daban.


Karanta : Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Waec A Sakon Message

Ina Fatan Masu Tambayoyi Akan Direct Entry (DE) yanzu Sun Samu cikakkiyar Amsar Su?

Mungode Musha Ruwa Lafiya Daga National Coordinator Shehu R. Na'Allah.

Domin aikowa da tambaya ko Neman Karin bayani Ku nememu a:

Arewastf@gmail.com

Call/Kira:- 08088119753



WhatsApp:- 08038485677


Daga Ni Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.


Rubutuka Masu Alaka :

Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb A Sakon Message


 Yadda Zaka Gane Idan Anyi Maka Uploading Din O'Level Result dinka A Portal Din Jamb


 Madannai 9 Da Zaka Iya Amfani Dasu A Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu

   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu. Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu   Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).   Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,   Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi. Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb   Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Z...

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta NECO

    Biyo bayan Sakin Sakamakon Jarrabawar NECO da Hukumar Shirya Jarrabawar tayi Shiyasa wannan Shafi Na Pandancy yaga Dacewar Yayi Rubutun da Zai nunawa Dalibai Hanyar da Yakamata Subi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu Cikin Sauki batareda shan wasu Wahalhalu ba,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar taka ta NECO sune :   Karanta : Tarihin Hukumar Jamb •> Da farko kashiga Browser din wayarka Sai Kadanna Gurin Bincike (Search) Sai karubuta Adireshin result.neco.gov.ng, Sai kadanna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken •> Bayan Shafin Yabude Zai Baku wasu Akwatina Guda Hudu, Akwati ta Farko An Rubuta Exam Year, Abinda Ake Bukatar kasanya a cikin wannan Akwati shine Shekarar da karubuta Jarrabawar taka ta NECO Misali 2020, ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zakuga An rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shine wacce Irin Jarrabawa kakeson Dubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External Novemb...