Skip to main content

Yadda Zaka Bude Asusun Ajiya Na Bankin Zenith Akan Wayarka Ta Hannu





   Tabbas Bankin Zenith ya banbanta da sauran Bankunan Kasarnan, Domin kuwa shine Bankin da yasauwakewa jama'a wahala da turereniyar Bude Account wato Asusu, tahanyar baiwa Al'umma damar Bude Asusun daga Gida ta hanyar yin amfani da wayarsu ta hannu.


Karanta : Yadda Zaka Bude Profile Tareda Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta Jamb Akan Wayarka Ta Hannu


  Hakika Ba Dolene sai ka mallaki Babbar wayaba kafin yin Wannan aikin (komai kankantar wayarka Zaka Iya Bude Asusun da ita cikin sauki).


  Kasani basai kanada kudi a layinka Zaka Iya Bude Asusun ba, A'a ko da babu ko sisi a Asusun wayarka, Zaka Iya Bude Asusun Bankin na Zenith,


  Sannan haka zalika koda bakada kudin sakawa a Asusun a Wannan lokacin Zaka Iya budewa, domin kuwa Zero Account ne, Ma'ana Zaka Iya cire Dukkanin kudin Asusun kabarshi babu ko sisi.


Karanta : Madannai 9 da Zaka Iya Amfani dasu a Madadin Mouse Lokacin Jarrabawar Jamb


  Ga Matakai 9 da zakabi domin Bude Asusun ajiyartaka na Bankin Zenith.



> Abinda zakayi da farko shine ka Danna lambobin *966*0# akan wayarka ta hannu

>Daganan zai kaika wani Guri da zakaga zabi kamar haka:

1> Open Account for Self

2> Open Account for 3rd Person


  Idan kanka Zaka budewa Asusun sai kayi Reply da 1, Idan kuwa wani Zaka budewa saika Danna Lamba 2.


>Daganan zaikaika wani guri da zai baka zabi guda biyu:


Did want Open Account with your BVN number ?

Yes
No


  Idan kanada Lambar BVN saika zabi Yes, Idan kuwa bakada ita sai kazabi No.


  Idan kazabi cewar kanada BVN zai kaika wani Guri da Zaka rubutata, sannan zai kaika gurin da Zaka rubuta ranar haihuwarka,

 Idan kuwa kazabi cewar bakada ita to zai kaika wani guri da zai baka zabin


1> Continue

2> Cancel


  Sai ka zabi Continue, wato zabi na farko.


> Daganan zaikaika wani guri da zakaga an rubuta Enter Surname (Ma'ana suna nufin ka rubuta sunan Mahaifinka),



> Bayan ka rubuta sunan Mahaifinka ka tura, zai kaika wani gurin kuma da zakaga an rubuta Other names maximum of two names (Ma'ana ka rubuta sunanka sannan Idan Kana amfani da sunan Kakanka ko Sunan Garinku anan Zaka rubutashi, bayan ka rubuta sunanka),

> Bayan kadanna mabullin Send, daganan zai kawoka wani guri da zakaga an rubuta Enter preferred Branch Number. Enter 0 If you don't have (Ma'ana kasaka lambar Reshen Bankin da Kake Bude Account din a gurin, kasaka 0 Idan bakadashi) to a matsayinka na Wanda yake Bude Account din daga Gida Kamata yayi kayi Reply da 0, domin kuwa bakada wata Branch Number,

  Amma Idan kasan Lambar Reshen Bankin Zenith mafi kusa daku (Ma'ana inda kakeson zuwa domin ayi maka Activating din Account din naka Zaka Iya sakata), Misali Lambar Reshen Bankin Zenith na WUDIL a Jihar Kano itace 234 sai ka sakata.


  To da zarar ka kammala bin wadancan matakai da muka lissafo👆 shikenan shikenan ka Bude Account (Asusu) a Bankin Zenith, zasu turo maka Account Number Dinka,


 Daganan za'a Iya turo maka Kudi a Account din naka, amma bazasu Fitaba.



Karanta : Yadda Zaka Gane Idan Anyi Maka Uploading din O'level Result Dinka A Portal din Jamb


   * To Yaza'ayi Kudin Su fita ?


   Abinda zakayi shine, Bankin Zenith sun baka Tsawon watanni 3, Ma'ana kwanaki 90, domin ka ziyarci Bankin Zenith ayi maka Activating dinsa, sannan Idan ma bakada BVN za'ayi maka, sannan kuma za'a baka ATM, daganan Zaka Iya saka kudi kuma Zaka Iya cirewa.


• To amma dame - dame ake bukatar naje Bankin na Zenith ?


   Abubuwan da ake bukatar kaje dasu Sune :


•Valid I.D card (National I.D Card, or Voter's Card e.t.c.)

• Nepa Bill.


 Idan kaje za'a baka Form ka cike daganan za'ayi maka BVN, kuma za'a baka ATM card.


     Ya Amfaneka ?


Danna Mabullin Share domin Sauran Abokanka suma Su Karu.



   Nagode



    Miftahu Ahmad Panda.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Yadda Zaka Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar NECO Na Token Code

   Tun lokacin da Hukumar NECO ta Canja tsarin yadda Ake Duba Sakamakon Jarrabawar Daga yin Amfani da Scratch Card Zuwa yin Amfani da Token Code, Dalibai da Dama Sun shiga Tsilla-Tsillar kasa Duba Sakamakon jarrabawoyinsu bisa rashin Sanin Yanda Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu ta NECO a shafin Hukumar, Hakanne Yasanya Wannan Shafi Naku Mai Farin Jini Na Pandancy Yayi rubutu akan Yadda Dalibai Zasu Sayi Lambobin Duba Sakamakon Jarrabawar ta NECO a shafinta Cikin Sauki,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin sayen Lambobin Na Token Code sune Kamar haka :   Karanta : Tarihin Hukumar NECO •> Dafarko kaziyarci shafin Duba Sakamakon Jarrabawa na Hukumar ta NECO akan Adireshin  result.neco.gov.ng, •>Bayan shafin Yabude Sai katafi Kasansa Gurin da Zakaga An rubuta Purchase Token a zagaye da koriyar Kala, Sai kadanna Shi, •> Bayan Yabude zai baka damar kasanya Email Address da Password dinka, to a matsayinka Na Sabon Wanda Zai Sayi W...

Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka Ta NECO

    Biyo bayan Sakin Sakamakon Jarrabawar NECO da Hukumar Shirya Jarrabawar tayi Shiyasa wannan Shafi Na Pandancy yaga Dacewar Yayi Rubutun da Zai nunawa Dalibai Hanyar da Yakamata Subi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar tasu Cikin Sauki batareda shan wasu Wahalhalu ba,     Saukakan Matakan da Zakabi Domin Duba Sakamakon Jarrabawar taka ta NECO sune :   Karanta : Tarihin Hukumar Jamb •> Da farko kashiga Browser din wayarka Sai Kadanna Gurin Bincike (Search) Sai karubuta Adireshin result.neco.gov.ng, Sai kadanna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken •> Bayan Shafin Yabude Zai Baku wasu Akwatina Guda Hudu, Akwati ta Farko An Rubuta Exam Year, Abinda Ake Bukatar kasanya a cikin wannan Akwati shine Shekarar da karubuta Jarrabawar taka ta NECO Misali 2020, ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zakuga An rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shine wacce Irin Jarrabawa kakeson Dubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External Novemb...